Kungiyar addinai ta Najeriya NIREC a ranar Juma’ar nan ta tabbatar da zaman lafiya a kasar, inda ta ce babu wani addini da ya fi wani addinin.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa A yayin da ta ke tabbatar da cewa Najeriya kasa ce mai yawan addinai a karkashin Ubangiji, kungiyar ta yi kira ga malaman addini da su kauracewa siyasantar da al’amura da ka iya haifar da rikici.
NIREC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya Daniel Okoh da shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya Alhaji Muhammed Sa’ad Abubakar III suka fitar.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Shugabannin ba NIREC sun ce sun damu matuka da irin halin da ake ciki na kalaman nuna kiyayya kafin da kuma bayan zaben 2023.
KARANTA WANNAN Zaben 2023 Ba Zai Saka Naijeriya Cikin Rikicin Addini Ba – Sultan
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Sanarwar ta ce, “Rikicin addini don son zucuya, siyasa na iya haifar da rikicin addini a Najeriya. Don haka NIREC ta yi Allah wadai, da kakkausar murya, maganganun da ke nuna cewa addini daya ya fi wani addini.
“NIREC ta tabbatar da cewa Najeriya kasa ce mai yawan addinai a karkashin Ubangiji. Muna fata duk da haka kowane dan Najeriya zai iya zama Kirista na gaskiya ko kuma Musulmi na gaskiya domin hakan zai inganta dabi’un addini da za su iya canza al’umma.
“Ganin cewa galibin ’yan siyasa a Najeriya suna yin addini daya ko Fatan , ya kamata ‘yan siyasa Kirista da Musulmi su rika shelanta tsoron Allah da kaunarsa ta hanyar kula da zaman lafiya da jin dadin ‘yan kasa.
“NIREC ta yi kira ga shugabannin addinai da su guji yin amfani da addini a siyasance wanda zai iya haifar da rikici. Muna Allah wadai da masu ra’ayin ‘yan siyasa wadanda babban burinsu shi ne cimma burinsu na siyasa ta kowace hanya da suka hada da amfani da addini a matsayin abun fakewa.
” NIREC ta yi kira ga shugabannin siyasar mu da su yi amfani da dandamalin su wajen kai zaman lafiya, hadin kai da zaman lafiya tare da kaurace wa yin kalamai ko tsokaci da za su iya ta’azzara zafafan siyasar da al’umma ke ciki.
“NIREC tana kira ga duk ‘yan siyasa da su yi siyasa da tsoron Allah cikin mutunci da adon su ta hanyar nisantar siyasar rarrabuwar kawuna da bangaranci.
“NIREC ta yi kira ga al’umma da su lura cewa an kammala zabe kuma kararraki daban-daban suna gaban kotu suna kalubalantar sakamakon da aka samu don haka dole ne a baiwa bangaren shari’a damar gudanar da ayyukansu.
“Dole ne ‘yan Najeriya su ci gaba da zama masu kishin kasa, masu bin doka da oda don samun zaman lafiya, kuma su yi adawa da duk wani makirci da magudi na shugabannin da ke amfani da addini wajen wargaza al’umma.
“Mu yi addu’a ga al’ummar da za ta ci gaba da inganta adalci da zaman lafiya. Aikin gina Najeriya mai albarka aikin kowane dan kasa ne. Allah ya albarkaci Tarayyar Najeriya!”
A Wani Labarin Kuma Gwamnan Kano Yayi Wasu Sabbin Naɗe-naɗe
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin Sakataren Yada Labarai na Mataimakin Gwamna Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Ibrahim ya kammala karatunsa na adabi a harshe turanci a jami’ar Bayero ta Kano.