Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya nada kwamishinoni 19 da ‘yan majalisar zartarwa na jihar, bisa amincewar majalisar dokokin jihar, Daily Trust ta rawaito.
Daga cikin su akwai Hon. Ali Haruna Makoda, tsohon shugaban ma’aikata na tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, da Hon. Nasiru Sule Garo, yaya ga Murtala Sulen Garo mataimakin dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben 2023.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Yiwa Sabon Mukaddashin IGP Ado
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika jimillar sunaye 19 ga majalisar domin tantance su.
Kakakin majalisar, Hon. Jibril Ismail Falgore, ya fitar da jerin sunayen yayin da yake karanta wasikar a zauren majalisar ranar Talata.
Bayan karanta kudirin nadin da shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawal Hussaini Chediyar Yangurasa (Dala) ya gabatar, wanda Hon. Tukun Muhammad (Fagge) a matsayin na biyu.
Sannan an bukaci wadanda aka nada su bayyana a gaban majalisar a ranar Laraba domin tantance su.
Wasikar ta kara da cewa, “A bisa ga ikon da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya ba ni, ina so in mika jerin sunayen da ke kasa a hukumance domin nada kwamishinoni don neman amincewar majalisar dokokin jihar Kano.
“Cikakkun jerin sunayen wadanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika wa majalisar dokokin jihar Kano a matsayin mukamin kwamishinoni.”Gasu kamar haka
1- Comrade Aminu Abdulsalam
2- Hon. Umar Doguwa
3- Hon. Ali Haruna Makoda
4- Hon. Abubakar Labaran Yusuf
5- Hon. Danjuma Mahmoud
6- Hon. Musa Shanono
7- Hon. Abbas Sani Abbas
8- Hajiya. Aisha Saji
9- Hajiya. Ladidi Garko
10- Dr. Marwan Ahmad
11- Engr. Muhd Diggol
12- Hon. Adamu Aliyu Kibiya
13- Dr. Yusuf Kofar Mata
14- Hon. Hamza Safiyanu
15- Hon. Tajo Usman Zaura
16- Sheikh Tijjani Auwal
17- Hon. Nasiru Sule Garo
18- Hon. Haruna Isa Dederi
19- Hon. Baba Halilu Dantiye
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: A Karon Farko, Shugaba Tinubu Ya Bar Najeriya Zuwa Turai Domin Halartar Taro
Shugaban kasa Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa birnin Paris domin halartar taron Paris kan Sabuwar Yarjejeniyar Kuɗi ta Duniya
Wannan itace ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje a matsayin shugaban kasa
Shugabannin za su yi la’akari da damammaki na maido da harkokin kudi ga kasashen da ke fuskantar kalubalen kudi na gajeren lokaci