Yanzu haka dai babbar kotun tarayya da ke da matsiguni a Abuja ta bayar da belin dakatacce mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, Punch ta rawaito.
A ranar Alhamis ne mai shari’a James Omotosho ya bayar da belin Kyari da wasu ‘yan uwansa biyu – Baba Kyari da Ali Kyari bisa tuhumar su da laifin kin bayyana kadarori ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.
KARANTA WANNAN: Ma’aikatan Wata Jiha a Arewa Sun Bada Sharadi Kafin Su Dakatar da Yajin Aiki
Da yake yanke hukunci a karar da wanda ake kara ya shigar, mai shari’a James Omotosho ya bayar da belin Kyari a kan tsabar kudi naira miliyan N50m tare da mutum biyu wadanda zasu tsaya masa.
Mai shari’a Omotosho ya kara da cewa, dole ne wadanda za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarorin da suka kai naira miliyan N25m a karkashin ikon wannan kotun.
Sauran sharuddan sun hada da cewa Kyari da wadanda za su tsaya masa za su ajiye fasfo dinsu na kasa da kasa, da bayanan asusunsu, da takardun mallakar kadarori na wadanda za su tsaya masa da kuma hotunan fasfo din su na baya-bayan nan a gaban rijistarar kotun.
Baya ga haka, alkalin ya kara jaddada amincewar sammacin sakin sa ga abubuwan da ke faruwa a wata shari’ar da ke gaban mai shari’a Emeka Nwite inda ake tuhumarsa da wasu mutane hudu kan laifukan da suka shafi muggan kwayoyi.
Da yake amsa bukatarsa, alkali ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa yana da hatsarin barin kasa kuma ba zai ki halartar shari’ar da ake yi masa ba.
Mai shari’a ya yi nuni da cewa NDLEA ba ta musanta ikirarin Kyari na cewa yana gidan yarin Kuje a lokacin da aka fasa gidan yarin da ya gabata ba, amma bai tsere ba ko da ya samu dama.
“Akan yiwuwar wanda ake tuhuma na 1 ya halarci zaman shari’ar da ake yi masa, ya dace a bayyana cewa, kamar yadda takardar da ke goyon bayan bukatar ta nuna, mai neman ya bayyana cewa yana tsare a gidan yarin Kuje lokacin da aka kama shi a gidan yari a ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2022.
“Ya tsaya a wurin, duk da ya samu damar tserewa.
“Wanda ya shigar da kara bai kalubalanci wannan tuhume-tuhumen wanda ke nufin an shigar da shi ba.
“Wannan ya nuna cewa mai nema bai yarda ya gudu daga shari’ar da ake yi masa ba kuma ya nuna niyyar zuwa kotu idan an buƙata.
“Wannan batu zai yi tasiri ga mai nema, ta yadda hakan ya zama shaida ga kotu cewa mai neman ba zai tsallake sharudan beli ba idan aka ba shi.
“Na lura cewa an yi hukunce-hukuncen hana wanda ake tuhuma/mai nema beli na 1.
Ƙari ga haka, ya ce laifukan da aka tuhumi Kyari da waɗanda ake tuhumarsa da su abu ne na beli.
“Bai aikata wani laifin kisa ba kuma ba a tabbatar da cewa yana da hadarin barin kasa ba. Ni, saboda haka, ina amfani da hankalina don goyon bayan wanda ake tuhuma / mai nema.”
Kotun ta dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 18 ga watan Oktoba.
A wani labarin kuma, Mmesoma: Ku Dakatar Da Daukar Duk Wani Matakin Ladabtarwa – Majalisar Wakilai ga JAMB
Majalisar wakilai ta kuduri aniyar bijirewa sakamakon jabun makin jarabawar kammala manyan makarantu (UTME) da Ejikeme Mmesoma ta yi.
An cimma matsayar ne a ranar Laraba bayan wani kudiri da Awaji-Inombek Abiante ya gabatar a zauren majalisar.