Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta tsayar da ranar Laraba 20 ga watan Satumba, 2023, domin yanke hukunci kan karar da jam’iyyar APC ta shigar kan Gwamna Abba Yusuf na jam’iyyar, NNPP, Daily Post ta rawaito.
Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, shugaban kwamitin mutane uku, ya ce za a yanke hukuncin ne kafin kwanaki 180 da doka ta ba su.
KARANTA WANNAN: Kano: Kotun Zabe ta Tabbatar da Nasarar Zaben dan Majalisar NNPP
Dage zaman kotun ya biyo bayan jawaban karshe da bangarorin biyu suka yi.
Yayin da ta ke gabatar da jawabi na karshe ga kotun, APC ta bukaci kotun da ta tabbatar da karar da ta shigar ta kuma mayar da Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
INEC, NNPP da Yusuf sun bukaci kotun da ta yi watsi da karar.
A wani labarin kuma, Wata Mata Ta Roki Kotu Ta Sanya Mijinta Ya Tsinke Igiyar Aurensu
Wata ‘yar kasuwa, Anthonia Ubong ta roki wata kotun kwastomari da ke zaune a Jikwoyi, data raba auren su da mijinta Ime Prayer bisa dalilin tashin hankalin cikin gida.
Ubong ta gabatar da bukatar ne a ranar Litinin domin kare kanta a karar data shigar da Ime.
“Mijina ba ya ba ni abinci. Ya murguda kafata a lokacin da na ce ya ba ni Naira 100 in saya abinci a lokacin ina da ciki wata takwas.
“Raunin da ke jikin kafata bai daina ciwo ba har sai da na haifi jaririna.
“Ya kuma ki biyan Naira 60,000 na tiyatar da aka yi na haifi jaririna bayan na yi doguwar nakuda.