Kakakin Majalisar Wakilai, Honarabul Abbas Tajudeen, ya bayyana alhininsa kan mutuwar mutum daya sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu sassan mazabar Kosofe dake Jihar Legas.
Kakakin majalisar a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Musa Krishi ya fitar, ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ambaliyar ta raba mutane sama da 2,000 da gidajensu.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Peter Obi Ya Shigar da Kara a Kotun Daukaka Kara
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa ambaliyar ta shafi wata makaranta, inda ta koma wani gini mai dakuna 500, wanda aka fi sani da Agboye Estate, Oduntan Street dake Ketu, a Ikosi-Isheri LCDA ta jihar Legas.
Ginin ya fado ne a ranar Asabar bayan ruwan sama da aka kwashe sa’o’i da yawa ana yi wa mafi yawan sassan jihar.
Dangane da haka, Shugaban Majalisar ya yi kira ga hukumomin tarayya da na Jiha da abin ya shafa da su dauki matakin dakile sake afkuwar irin wannan lamari.
Abbas ya bukaci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta gaggauta samar da matakan da suka dace ga ‘yan gudun hijirar.
Shugaban majalisar ya yabawa shugabar kwamitin harkokin mata da ci gaban al’umma ta majalisar Hon. Kafilat Ogbara, saboda bayar da matsuguni ga ‘yan gudun hijirar, wadanda suka fito daga mazabarta.
A martanin da ta mayar dangane da bala’in, Ogbara ta bayar da gudunmuwar wani gida mai dakuna 10 ga mazaunan, wanda ya kasance ofishin mazabarta, domin iyalan wadanda abin ya shafa, musamman yara, su samu mafaka.
Shugaban majalisar ya ce labarin alherin Ogbara abin mamaki ne, yayin da ya yaba wa ‘yar majalisar kan yadda ta nuna jagoranci ta hanyar misali.
A wani labarin kuma,Gwamnatin Nasarawa Za ta Duba Shari’ar Fursunonin da Ake Tsare Dasu Ba Bisa Ka’ida Ba – Babban Lauya
Babban Lauyan jihar Nasarawa kuma kwamishinan shari’a, Labaran Magaji a ranar Talata ya bayyana cewa gwamnatin jihar a shirye take ta sake duba shari’ar fursunonin da aka tsare ba bisa ka’ida ba da nufin ‘yantar da su kamar yadda doka ta tanada.
Babban Lauyan wanda ya bayyana hakan a garin Lafiya a lokacin da wakilan kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar Nasarawa suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.
Kamishinan ya kuma shawarci jama’a da su ci gaba da bin doka da oda. da rashin cin karo da doka, don gujewa kamawa da tsare su a wuraren da ake tsare da su.