Jam’iyyar APC reshen jihar Ondo a ranar Talata ta dauki wani mataki mai tsauri a kan shugaban jam’iyyar na maza ta 1 na karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma, Olumide Awolumate bisa laifin cin zarafin kwamishiniyar mata a jihar Olubunmi Osadahun.
Jam’iyyar ta dakatar Awolumate ne har sai baba tagani biyo bayan harin da ya kai wa kwamishiniyar a kan rabon kayan tallafin rage radadi a karamar hukumar.
KARANTA WANNAN: Hukuncin Kotun Zabe: FRSC ta Gargadi Magoya Bayan Jam’iyyu Su Guji ‘Bikin Amutu Ko Ai Rai’
Dakatar da shugaban mazabar da aka yi ya biyo bayan rigingimun jam’iyyar ne a Akoko ta arewa maso yamma, daga bisani kuma ta sanar da shugaban jihar, Ade Adetimehin.
An yanke hukuncin dakatar da Awolumate ne saboda rikicin da ya barke tsakaninsa da Osadahun a kwanakin baya, wanda ya jawo hankulan jama’a da kuma tofin Allah tsine.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar, Alex Kalejaye ya fitar, ya bayyana cewa jam’iyyar reshen karamar hukumar ta yi aiki bisa umarnin da sakatariyar jihar ta bayar.
Ya ce sakatariyar jam’iyyar ta jihar ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, kuma dakatarwar da aka yi wa Awolumate daga baya an dauki matakin da ya dace.
Lamarin wanda ya faru a karshen mako, an dauki hoton bidiyo ne da aka yada a shafukan sada zumunta.
Hotunan sun nuna shugaban mazabar, wanda aka fi sani da ‘Cuba’, yana da hannu a wani harin ta’addanci ga Osadahun.
Bidiyon da aka yi ta yadawa ya tayar da hankalin jama’a tare da neman a gaggauta daukar matakin ladabtarwa kan jami’in jam’iyyar da ya yi kuskure.
“Shugaban jam’iyyar a Akoko ta arewa maso yamma na ganin ya dace a sanar da sakatariyar jiha a hukumance cewa an dakatar da Awolumate Olumide daga jam’iyyar har zuwa wani lokaci a Akoko ta arewa maso yamma na babbar jam’iyyar mu.
“Injiniya Adetimehin, da ya samu takardar dakatarwar, ya bada tabbacin cewa sakatariyar jihar za ta kafa wani gagarumin kwamitin ladabtarwa nan take domin ganin an hukunta Awolumate da aka dakatar da kuma zama tamkar hana wasu shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar. “
A wani labarin kuma, An Hana ‘Yan Jarida Shiga Kotu, Yayin Da Za’a Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Bauchi
An hana ‘yan jarida shiga harabar babbar kotun jihar Bauchi inda kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Bauchi za ta yanke hukunci a yau.
An hana ‘yan jarida dake wakiltar kungiyoyin yada labarai daban-daban shiga cikin kotun domin gabatar da shari’ar da hukuncin kotun.