Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Laraba ya yi alkawarin samar da isassun kudade don ilimi a cikin kasafin kudin jihar, Daily Post ta rawaito.
Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a wajen bikin yaye dalibai na kwalejin fasaha da kimiya ta Zamfara, ZACAS karo na 23 a Gusau babban birnin jihar.
.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Tsige Abba Gida-Gida, Ta Faɗi Wanda Ya Ci Zaben Gwamnan Kano
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, ZACAS ta kunshi Makarantar Fasahar Kimiyya, Nazarin Shari’a, Makarantar Art and Humanities, Makarantar koyon aikin jarida, da Makarantar Preliminary Studies.
Sassan sanarwar sun ce, “Bikin karramawar ya yi nuni da daukar sabbin dalibai 2,369 da suka samu shiga makarantar a zangon karatu na shekarar 2023/2024.
“Gwamnan ya bayyana cewa, dimbin daliban da makarantar ta yaye a tsawon shekaru suna yin tsokaci ne kan yadda kwalejin ke gudanar da ayyukanta.
“Gwamnan ya yi alkawarin samar da ingantaccen ilimi mai inganci ga daukacin mazauna jihar Zamfara, ba tare da la’akari da yanayin zamantakewar al’umma ba, daidai da manufofin ci gaban al’umma kan ilimi.
“Ya bayyana jin dadinsa kan irin namijin kokarin da kwalejin ke yi na samar da damammaki ga matasa, ya kara da cewa gwamnatinsa za ta magance kalubalen da ke fuskantar manyan makarantun da suka hada da kudade, dakunan gwaje-gwaje da tantancewa, da kuma inganta tsarin hukumomi.
“A wani bangare na kudurin gwamnatinsa na ba da fifiko kan ilimi, Gwamna Lawal ya tabbatar da aniyarsa ta saka hannun jari sosai wajen inganta ababen more rayuwa da sauran kayan aikin koyo a dukkan manyan makarantun.”
Tun da farko, shugaban kwalejin fasaha da kimiyya ta Zamfara ZACAS, Dakta Yakubu Sani, ya yabawa gwamnan bisa kasancewarsa wanda ya fi kowa bayar da guraben karo karatu a shekaru goma da suka gabata.
Sanarwar ta kara da cewa, “Shugaban kwalejin ya yarda cewa a cikin shekaru goma da suka gabata, gwamnan yana bayar da tallafin karatu ga dalibai sama da 200 na ZACAS a duk shekara.”
A wani labarin kuma, Ba Abu Ne Mai Sauki Ba Maye Gurbin de Gea – Onana
Mai tsaron ragar Manchester United, Andre Onana, a ranar Talata, ya ce maye gurbin tsohon mai tsaron gida, David de Gea, “ba abu ne mai sauki ba.”
Da yake magana a wani taron manema labarai gabanin karawar da za su yi da Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba, dan Kamarun mai shekaru 24, ya yi ikirari, inda ya kara da cewa yana da kwarin gwiwar wasan da kungiyarsa za ta yi a sauran kakar wasa ta bana.