- Gwamnatin Kano ta dage dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya don dakile tabarbarewar doka da oda a jihar
- Sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a jihar ya biyo bayan hukuncin da kotun zabe ta yanke na tsige Abba Yusuf a matsayin gwamna
- Nan take Kotun ta tabbatar da Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar
Gwamnatin Kano ta dage dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya don dakile tabarbarewar doka da oda a jihar.
A ranar Laraba ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a jihar biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na tsige Abba Yusuf a matsayin gwamna.
KARANTA WANNAN: Kotun Zabe Ta Kwace Kujerun Yan Majalisa 3 Na PDP, Ta Miƙa Wa APC da LP
A hukuncin da kotun ta yanke tun farko ta hanyar Zoom, kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta baiwa Yusuf.
Kotun ta kuma tabbatar da Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar.
Jim kadan bayan yanke hukuncin, an fara fargabar yiwuwar wata zanga-zangar da magoya bayan gwamnan za su yi a fadin Kano.
Sakamakon haka, Muhammad Gumel, kwamishinan ‘yan sanda na Kano, ya ce an tura jami’an tsaro a fadin birnin domin tabbatar da dokar hana fita.
Sai dai da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Halilu Dantiye, kwamishinan yada labarai na Kano, ya ce an dage dokar hana fita ne domin baiwa mazauna jihar damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Dantiye ya kuma bukaci mazauna jihar da su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A wani labarin kuma, Zaben Gwamna: CSOs sun Gargadi dan Takarar Jam’iyyar SDP kan Nuna Kabilanci
Gamayyar Kungiyoyin fararen hula akalla 25 ne suka yi kira ga hukumomin tsaro da su ja kunnen jam’iyyun siyasa kan ayyukan da ka iya jefa jihohin Bayelsa,Imo, da kuma Kogi cikin mawuyacin hali
Ya zama wajibi a dauki mataki kan wadannan ayyuka domin dakile yiwuwar tabarbarewar tsaro da kalaman da ka iya haifar da rashin jituwar kabilanci
Jam’iyyar SDP ta yi kaurin suna a jihar wajen furta kalaman da basu dace ba da ya kamata hukumomin tsaro su gargadi masu ruwa da tsaki
Gamayyar Kungiyoyin fararen hula akalla 25 ne suka yi kira ga hukumomin tsaro da su ja kunnen jam’iyyun siyasa kan ayyukan da ka iya jefa wasu jihohi cikin mawuyacin hali, gabanin zabukan gwamnonin jihohin Bayelsa, Imo da kuma Kogi.
Kungiyoyin farar hula, a cikin sanarwar da suka fitar bayan share tsawon kwanaki uku ana gudanar da zabukan jihohin uku, ta yi nuni da yadda jam’iyyar Social Democratic Party SDP ta yi kaurin suna a jihar Kogi a matsayin misali na abin da ya kamata hukumomin tsaro su gargadi masu ruwa da tsaki.