- Gwamnatin Bauchi a ranar Juma’a ta gabatar da kayayyakin abinci a matsayin tallafi ga ‘yan adawa a jihar
- An dauki wannan matakin ne domin ganin dukkan bangarorin al’umma sun ci gajiyar wannan shiri
- An bukaci shugabannin matasan jam’iyyun adawa su tabbatar da cewa matasan su sun ci gajiyar wannan kayayyakin
Duba da yadda cire tallafin man fetur ya janyo wa dukkan ‘yan Najeriya wahalhalu ba tare da la’akari da kabilanci da addini da siyasa ba, gwamnatin jihar Bauchi a ranar Juma’a ta gabatar da kayayyakin abinci a matsayin tallafi ga ‘yan adawa a jihar.
‘Yan jam’iyyar APC da NNPP da sauran su, an ba su kayayyakin ne a matsayin nunin gudanar da mulkin dunkulewar gwamnatin PDP.
KARANTA WANNAN: NMA ta Tabbatar da Sace Wani Likita
Wannan ci gaban dai ya yi daidai da alkawarin da gwamnan jihar Sen Bala Mohammed Abdulkadir ya yi na bai wa jam’iyyun siyasa na adawa kason su na kayayyakin jin dadin rayuwa da ya ce na dukkan ‘yan Najeriya ne.
An gabatar da kayayyakin ne ga galibin matasan ‘yan jam’iyyar adawa a fadin jihar.
Kwamishiniyar jin kai da Agajin Gaggawa ta Jiha Hajara Yakubu Wanka, Itace wadda ta gabatar da kayayyakin a madadin Gwamnan ta ce an dauki wannan matakin ne domin ganin dukkan bangarorin al’umma sun ci gajiyar wannan shiri.
Ta ce tun daga nan ne Gwamnan ya umarci kwamitin da ya tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa na adawa sun samu nasu kason na kayayyakin jin kai.
Ta kuma tuhumi shugabannin matasan jam’iyyun adawa da suka hada da APC da NNPP da sauran su da su tabbatar da cewa matasan su sun ci gajiyar wannan kayayyakin.
Hajara Yakubu Wanka ta yi alkawarin raba duk wani kayan tallafin rage radadi don mutane su amfana.
Shugaban matasan jam’iyyar APC, Ibrahim Ago ya mayar da martani a madadin jam’iyyun adawar da suka karbi kayayyakin yayin da ya gode wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohamed bisa wannan karimcin tare da yin alkawarin tabbatar da yadda aka raba kayayyakin.
Ya kuma yaba wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed bisa shigar da jam’iyyun adawa a cikin abubuwan kwantar da tarzoma ba tare da wani nuna bambanci ba, ya kuma yi addu’ar Allah ya saka masa da alheri.
A wani labarin kuma, EPL: Merson Ya Yi Hasashen Yadda Wasan Arsenal da Tottenham Zai Kasance
Paul Merson ya ce yana sa ran Arsenal za ta yi nasara a kan Tottenham Hotspur a karawarsu ta Premier ranar Lahadi.
Kungiyoyin biyu na Arewacin London dukkansu suna da maki 13 a wasanni biyar na farko.