- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kira taron gaggawa na tsaro bayan sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau
- Daukar matakin ya biyo bayan sace daliban da aka yi a daren Alhamis a gidansu
- Taron na da nufin ganin an sako duk wadanda aka sace cikin gaggawa da kuma samar da mafita mai dorewa kan matsalar rashin tsaro
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kira taron gaggawa na tsaro bayan sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau.
Taron majalisar tsaro na gaggawa ya zama tilas ne sakamakon sace daliban da aka yi a daren Alhamis a gidansu da ke kauyen Sabo Gida a karamar hukumar Bungudu.
KARANTA WANNAN: An Gurfanar da Mutane 2 a Gaban Kuliya Bisa Zargin Satar Koko
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Juma’a, ya jaddada cewa taron na da nufin ganin an sako duk wadanda aka sace cikin gaggawa da kuma samar da mafita mai dorewa kan matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da zama ruwan dare ga gwamnati.
Ya kara da cewa gwamnan ya umurci mataimakin gwamna Mani Mallam Mummuni da ya baiwa jami’an tsaro dukkan goyon bayan da suka dace domin dawo da zaman lafiya a duk yankunan da abin ya shafa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A yayin taron, shugabannin tsaro sun tabbatar wa mataimakin gwamnan kan kudirinsu na maido da zaman lafiya a jihar.
“Hakazalika sun tabbatar wa mataimakin gwamnan ba tare da wata shakka ba cewa sojoji sun yi nasarar ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su.
“Shugabannin tsaro sun kara tabbatar da cewa sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane da dama kuma suna ci gaba da bin su don tabbatar da ceto duk wadanda abin ya shafa.
“Mani Mallam Mummuni ya bukaci shugabannin hukumomin tsaro da su inganta kasancewar sojoji a yankunan da ba su da tabbas domin sa ido.
“Mataimakin gwamnan ya tabbatar wa al’ummar Zamfara cewa jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen ganin an shawo kan lamarin.
A wani labarin kuma, Majalisar Wakilai Ta Sanar da Ranar da Za ta Cigaba Da Ayyukan Majalisa
Majalisar Wakilai za ta dawo aiki da ga hutun ta na shekara domin ci gaba da zaman majalisar wakilai ta 10
Majalisa ta 10 ta tafi hutu ne a cikin watan Yuli, 2023, bayan kammala zaman da shugaban majalisar ya jagoranta
Kakakin majalisar ya shirya sanar da zaman wakilan kwamitoci
Majalisar Wakilai a ranar Talata 26 ga watan Satumba, 2023 za ta dawo aiki da ga hutun ta na shekara domin ci gaba da zaman farko na majalisar wakilai ta 10.
Magatakardar Majalisar Dokta Yahaya Danzaria ne ya sanar da hakan a cikin wasikar da ya aiko wa wakilimu a ranar juma’a.