- Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wata mata mahaifiyar ‘ya’ya biyu a gaban kotun majistare da ke Abuja bisa zarginta da sace wayoyin jama’a
- Matar da ake zargi da dogon hannun ta kasance mai sana’ar kwalliya
- Matar da ake zargi ta kware wajen shiga irin ta masu ibada yayin gudanar da ayyukanta na dogon hannu
Rundunar ‘yan sanda a ranar litinin ta gurfanar da wata mata mahaifiyar ‘ya’ya biyu a gaban kotun majistare ta Wuse Zone II, da ke Abuja, bisa zarginta da sace wayoyi a lokacin da take hidimar coci.
Matashiyar mai shekaru 26 da haihuwa, Chisom Nwogbo, wadda ta yi ikirarin cewa ita ce mai sana’ar kwalliya, tana fuskantar tuhuma biyu da suka hada da hada baki da kuma sata, zargin da ta musanta.
KARANTA WANNAN: FG ta Sanar Da Lokacin Da Za ta Fara Raba Kudade Ga ‘Yan Najeriya Miliyan 15
Dan sanda mai shigar da kara, Oyeyemi Adeniyi ya shaida wa kotun cewa wata Miss Esther Silas daga Mana Apartment, Dawaki, Abuja ce takai karar zuwa ga kwamishinan ‘yan sandan Abuja a ranar 13 ga watan Satumba.
Oyeyemi ya yi zargin cewa wanda ake kara a ranar 10 ga watan Satumba ta yi kama da mai ibada kuma ta je cocin Inspiration Life Community Church da ke unguwar Jahi a Abuja domin aikata laifin.
Ya kara da cewa Nwogbo ta saci wayoyi biyar da suka hadar da IPhone 14 Pro Max, Samsung Galaxy A32, iPhone X5, Techno Pop 5, da kuma wani samfurin Samsung Galaxy da baƙar jaka na mai ƙara da abokanta.
A cewarsa, yayin bincike, an gano wayoyin ne a Idu dake Abuja, inda aka kama wanda ake tuhuma.
Ya kuma bayyana cewa an gano bakar jakar hannu, da wayoyin Techno da kuma iPhones a yayin bincike a gidan wanda ake kara.
“Ta kuma shaida wa ‘yan sanda cewa ta sayar da sauran wayoyi ga wani mutum Paul, wanda aka fi sani da Daddy Fresh, wanda a halin yanzu yake hannun su.
“Wanda ake tuhumar ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta je majami’u daban-daban guda biyar a cikin FCT kuma ta sace wayoyin masu ibada ta hanyar amfani da irin wannan dabara,” in ji shi.
Oyeyemi ya ce daga baya an gano cewa an cire kudaden da suka kai Naira N150,000 da kuma Naira miliyan 1.3 daga asusunsu.
Ya kara da cewa, an kwato iPhone XS da Samsung wadanda kudinsu ya kai Naira miliyan 2 daga hannun wanda ake kara.
A cewar mai gabatar da kara, laifukan sun sabawa tanadin sashe na 97 da 288 na kundin laifuffuka.
Lauyan wadda ake kara, Ophie Ogheneyerowho, ya nemi a bayar da belin wanda yake karewa, inda ya bayyana cewa “wanda ake kara a halin yanzu tana reno jariri.”
Ya kara da cewa wanda ake tuhumar ya bai wa ‘yan sanda hadin kai a yayin gudanar da bincike tare da bayar da dukkan bayanan da ake bukata ba tare da wani bata lokaci ba.
Ya yi wa kotun alkawarin cewa wanda ake kara ba za ta tsallake sharudan bada belin ba idan har aka bayar da belinta, ya kara da cewa akwai amintattun wadanda za su tsaya a gaban kotu domin su tsaya wa wanda ake tuhuma.
Sai dai ya bukaci kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa a mafi sassaucin ra’ayi, yana mai tunatar da kotun cewa “wanda ake tuhuma ba ta da wani laifi har sai an tabbatar da ita da aikata laifin.”
Mai gabatar da kara bai ki amincewa da neman belin wanda ake tuhuma ba amma ya bukaci kotun da ta yi amfani da hankalinta cikin adalci.
Alkalin kotun, Izinyon Ibironke, ya shigar da karar wanda ake tuhuma da bayar da belinta a kan kudi naira miliyan biyu tare da mutane biyu da za su tsaya mata wadanda dole ne su mallaki abin dogaro da kai da kuma zama a karkashin ikon kotun.
Ta ba da umarnin cewa ma’aikatan kotun su tantance adireshin wadanda za su tsaya mata sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Oktoba da16 domin sauraren karar. NAN.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Kotu ta Tabbatar da Zaben Sanwo-Olu, Ta Yi Watsi da Karar Dan Takarar PDP
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Legas ta tabbatar da dawowar gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin zababben gwamnan jihar
A hukuncin da aka yanke kotun ta ce karar da PDP da dan takararta na gwamna suka shigar ba ta da wata cancanta
Tuni dai kotun zaben ta yi watsi da tambayar ko tana da hurumin sauraren karar
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Legas ta tabbatar da dawowar gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin zababben gwamnan jihar.
A hukuncin da aka yanke wanda mai shari’a Mikail Abdullahi ya karanta a madadin kwamitin mutum uku a ranar Litinin, kotun ta ce karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Olajide Adediran suka shigar ba ta da wani cancanta, don haka ta yi watsi da ita.