- Sufeto-Janar na ‘yan sanda IGP, Kayode Adeolu Egbetokun, ya gabatar da chekin kudi naira biliyan 1.3 ga iyalai 420 na ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki
- An bayar da wadannan kudaden ne domin rage wahalhalun da dangin mamacin ke fuskanta
- NPF ta tsaya tsayin daka
wajen bada fifiko domin kula da walwalar rayuwar kafatanin jami’anta
Sufeto-Janar na ‘yan sanda IGP, Kayode Adeolu Egbetokun, ya gabatar da chekin kudi naira biliyan 1.3 ga iyalai 420 na ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki a karkashin shirin tabbatar da rayuwa na rundunar, Tribune Online ta rawaito.
Da yake jawabi a wani takaitaccen biki da aka yi a hedikwatar rundunar da ke Abuja, IGP ya bayyana cewa, shirin “Group Life Assurance Plan,” tsarin jin dadin jama’a ne da aka kafa a sakamakon gyaran dokar ‘yan fansho ta shekarar 2004 a shekarar 2014 da ta samu kudade daga gwamnatin tarayya.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Najeriya da Benin Sun Rasa Damar Karbar Bakuncin Gasar AFCON 2027
Shugaban ‘yan sandan ya kara da cewa gabatar da shirin ya kuma kunshi tsarin inshorar jin dadin iyali na IGP.
Ya yi bayanin cewa shirin inshorar jin dadin iyali na IGP, “wanda rundunar ‘yan sandan Najeriya ke daukar nauyinta, an kafa ta ne a shekarar 2017 domin rage wahalhalun da dangin mamacin ke fuskanta kafin a biya kudin fansa.”
IGP ya ce cak din kudin ya kasance na shekarar 2021/2022 da kuma 2022/2023 ne.
Da yake karin haske, Egbetokun ya tunatar da cewa, “A ranar 14 ga watan Yuli, 2023, na samu damar bayar da tallafin kudi ga jimillar iyalai 68 na jami’an da suka mutu a bakin aiki.
“An kama wadannan mutane da kyau a karkashin Tsarin Tabbatar da Rayuwa na na ‘yan sanda 2022/2023. Jimlar cekin kudin da aka raba a lokacin bikin ya kai N535,618,788.44k.
“Bayanin da muka gabatar a yau ya kunshi raba cek din da ya kai N1,302,597,269.54k ga iyalai 420 da danginmu da suka rasu a matsayin fa’idar inshora na tsawon lokacin inshora na 2021/2022 da na 2022/2023 a karkashin tsarin tabbatar da rayuwa na manufofin kungiyar na shekarar 2021/2022 don Tsarin Inshorar Lafiyar Iyali na IGP.
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tsaya tsayin daka bisa imanin cewa kowane ran dan Adam yana da matukar amfani, kuma jin dadin jami’an mu shi ne babban abin da ke damun mu.
“Yunkurin da muka yi na ganin mun sauke nauyin da ya rataya a wuyanmu, da suka hada da samar da inshora da sauran fa’idoji ga jami’an da iyalansu da suka yi sadaukarwa ga al’ummomin da muke kauna, nuni ne na matukar godiya ga jajircewa da sadaukarwar jami’anmu.”
Wannan tallafi na zahiri, in ji IGP, zai taimaka wajen kara musu kwarin gwiwa tare da jaddada jajircewar da NPF ke yi wajen kyautata rayuwarsu da na iyalansu.
“Wannan shaida ce ta amincewa da sadaukarwar da suka yi da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da hidimarsu da daraja. Wannan gagarumin bukin da muke yi a yau shi ne mataki na farko a tafiyarmu,” inji shi.
Sai dai, ya ba da tabbacin cewa NPF za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan kudurin ta na kara inganta ayyukan jin kai ga dukkan ‘yan uwa na ‘yan sanda, ba tare da la’akari da matsayinsu ba – ko dai sun yi aiki sosai, ko sun yi ritaya ko kuma wadanda suka yi sadaukarwa ta karshe wajen gudanar da ayyukansu.
A cewar IGP, “Manufarmu ita ce samar da tallafin jin kai wanda zai tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar ‘yan sanda, tare da samar da yanayin da kowane jami’in ya ji ba wai kawai kima ba ne har ma da kare shi da kuma himma don isar da duk abin da ya dace wajen yi wa al’ummarmu hidima.”
IGP din ya kuma yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa da goyon bayansa na musamman wajen ganin an fitar da wasu manyan kudaden inshora.
Wannan karimcin, in ji shi, ba wai kawai ya nuna aniyar shugaban kasa na inganta jin dadin jami’ai da na ‘yan sandan Nijeriya ba ne, har ma ya bayyana kudirinsa na inganta tsarin tsaron cikin gida na kasarmu mai girma.
“Kokarin shugaban kasa zai kara sanya kwarin gwiwa ga mambobin rundunar yayin da suke gudanar da ayyukansu na doka tare da karfafa musu gwiwa don samun ingantacciyar hidima,” in ji shi.
A wani labarin kuma, NUJ ta Dakatar da Wasu Mambobinta 3 Saboda Rikicin Zabe
Sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) ta dakatar da wasu wakilanta uku daga dukkan ayyukan kungiyar har zuwa wani lokaci
Ofisoshin shiyyoyi na bukatar amincewar sakatariyar kasa kafin gudanar da taro
NEC ta yanke shawarar cewa babu wata majalisa da za ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) ba tare da amincewar Sakatariyar kasa ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada (Sashe na 4, 4 (a).
Sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) ta dakatar da wasu wakilanta uku daga dukkan ayyukan kungiyar har zuwa wani lokaci, bisa laifin kai kungiyar jihar Bauchi ta NUJ kara a kan harkokin zabe.
Wakilan da aka dakatar kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a ranar Talata, su ne Abdulwahab Muhammad, Garba Kabiru Abubakar, da Fatima Danjuma Idris.