- Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana kudurinsa na maido da martabar Najeriya data rasa ta fannin abinci
- Nan ba da dadewa ba Najeriya za ta shawo kan kalubalen karancin abincin da take fuskanta
- A halin yanzu gwamnati na aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da ke da nufin haɓaka ayyukan manona
Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana kudurinsa na maido da martabar da kasar nan ta yi hasararta ta fannin abinci.
Ministan wanda ya bayyana hakan a cikin sakon ranar samun ‘yancin kai, ya ce ya yi imanin cewa Najeriya za ta sake zama kan gaba wajen fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje, kamar yadda ta kasance a shekaru 60 zuwa 70.
KARANTA WANNAN: Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna A Jihar Nasarawa, Ta Lalata Gidaje Sama Da 60
Sanata Kyari yayin da yake mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya kan wannan muhimmin al’amari ya ba da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba kasar za ta shawo kan kalubalen karancin abinci da take fuskanta.
Ya yaba da gudummawar da kananan manoma ke bayarwa, wanda ya ce suna taka rawa wajen samar da abincin da al’ummar kasar ke amfani da su.
“Don tallafa wa waɗannan manoma, a halin yanzu gwamnati na aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da ke da nufin haɓaka ayyukansu.
“Mun gane kuma mun yaba da gudummawar da kananan matan karkara ke bayarwa ga samar da abinci na kasa,” in ji shi.
Ya jaddada kudirin gwamnati na samar da yanayi mai kyau da dacewa ga mata don kara yawan noman su da inganta zamantakewa da tattalin arziki.
A cikin karar da ya shigar, Kyari ya bukaci kungiyoyin kwadagon da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC suka wakilta da su sake duba shirinsu na tsunduma yajin aikin da za a yi a fadin kasar nan na sai baba ta gani.
Ya bayyana mummunan sakamakon da irin wannan yajin aikin zai haifar a halin da ake ciki tare da yin kira da a hada kai don magance matsalolin jin dadin ma’aikata.
Bugu da kari, ya bukaci manoma da masu ruwa da tsaki a harkar samar da abinci da su ci gaba da aikinsu ba tare da tsangwama ba. Ya jaddada cewa dakatar da noman zai yi tasiri sosai ga masu karamin karfi.
Ministan ya ce ya ci gaba da jajircewa wajen ganin an cimma wannan manufa da kuma tabbatar da ci gaba mai inganci ga bangaren noma na Najeriya.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Tsohon Gwamnan Kaduna Yero Ya Fice daga PDP
Tsohon gwamnan Kaduna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Mukhtar Yero ya yi murabus daga jam’iyyar
Tsohon gwamnan kafin daukar wannan mataki ya kasance dan jam’iyyar tsawon shekaru ashirin da suka gabata
Bayan mutuwar Yakowa a hatsarin jirgin sama, an rantsar da Yero a matsayin gwamnan Kaduna
Tsohon gwamnan jihar Kaduna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Mukhtar Yero ya yi murabus daga mukaminsa na jam’iyyar.
Murabus din nasa na kunshe ne a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu da kan sa kuma ya aika wa shugaban mazabar Kaura ta karamar hukumar Zariya mai kwanan wata 29 ga watan Satumba 2023.