- Jam’iyyar APC ta dakatar da yakin neman zaben gwamnan jihar Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamba
- Hakan ya biyo bayan samun rikici da ya yi sanadiyyar rasa rai
- Dan takarar gwamnan ya bayyana kaduwarsa bisa faruwar lamarin
Jam’iyyar APC ta dakatar da yakin neman zaben gwamnan jihar Kogi wanda za’a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba a matsayin girmamawa ga Ms Khadijat Yahaya, ‘yar jam’iyyar da ta mutu bayan wani hari da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai musu.
Mista Kingsley Fanwo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Lokoja.
KARANTA WANNAN: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar da Mutane 4 a Gaban Kotu Bisa Zargin Sace N5m
Ana zargin Khadijat ta rasa ranta ne bayan wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar SDP da na APC a Kotonkarfe a ranar 29 ga watan Satumba.
A halin da ake ciki, dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Usman Ododo, ya ziyarci iyalan marigayiyar a Kotonkarfe a ranar Talata domin jajanta musu bisa rasuwar ta.
Ododo ya bayyana kaduwarsa da rasuwar ta, sannan ya yi addu’ar Allah ya jikan ta.
Da yake mayar da martani, Malam Saliu Akawu ya godewa Ododo bisa wannan ziyarar.
Akawu ya ce halin da Ododo ya yi ya nuna cewa shi shugaba ne mai tausayin jama’ar sa.
Ya ce Khadijat mutuniyar ce mai son zaman lafiya wacce miyagun mutane suka yanke rayuwarta.
Ododo ya kuma ziyarci fadar Ohimege na Kotonkarfe, Alhaji Abdulrazak Koto, inda ya nuna alhininsa kan rasuwar Khadijat.
Ya bayyana ta a matsayin mace mai son zaman lafiya mai son ganin cigaba a Kotonkarfe tare da alkawarin tabbatar da adalci ga iyalan mamacin.
A wani labarin kuma,Hukuncin Kotu: Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Yi Wa’azin Hadin Kai Tsakanin Masu Ruwa da Tsaki
Shugaban Majalisar Dokokin Nasarawa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bukaci masu rike da mukaman siyasa na Gwamnan jihar da masu ruwa da tsaki da su ci gaba da mai da hankali domin samun ci gaba
Kada ku shagala da sukar ‘yan adawa,ku ci gaba da mai da hankali da yin aiki cikin hadin kai
Lokacin da masu rike da mukaman siyasa da sauran masu ruwa da tsaki suka yi aiki tare zai kawo ci gaba cikin sauri ba da zaman lafiya
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bukaci masu rike da mukaman siyasa na Gwamna Abdullahi Sule daga karamar hukumar Toto da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da mai da hankali da hadin kai domin samun ci gaba.
Ya kuma bukace su da su baiwa gwamnatin wannan rana goyon baya domin ci gaban jihar baki daya.