- Jam’iyyar NNPP ta Jihar Taraba, da dan takarar gwamna a zaben 2023, Farfesa Sani Yahaya, ya ce za su daukaka kara kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe
- Bayan hukucin kotun zabe gwamna da mataimakinsa sun gayyaci dan takarar gwamna da jam’iyyar NNPP domin ceto dukiyar jihar
- Tuni dan takarar Gwamna da NNPP suka sha alwashin ba za su huta ba har sai an yi adalci
Jam’iyyar NNPP ta Jihar Taraba, da dan takarar gwamna a zaben 2023, Farfesa Sani Yahaya, ya ce shi da jam’iyyarsa za su daukaka kara kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe.
A makon da ya gabata ne kotun ta yi watsi da karar da aka shigar a kan gwamnan jihar Dr Agbu Kefas na jam’iyyar PDP.
KARANTA WANNAN: PDP da Dan Takarar Gwamna Sun Garzaya Kotun Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Zabe
Yahaya da shugabannin jam’iyyar NNPP sun shigar da kara gaban kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar suna kalubalantar nasarar da gwamnan ya samu kan cewa an tabka magudi a zaben.
Da yake nuna rashin gamsuwa da hukuncin da aka yanke a wani taron manema labarai a ranar Laraba a Jalingo, babban birnin jihar, ya ce shi da jam’iyyarsa sun kammala shirin kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara da za ta zauna a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Ya ce, “Ba mu yarda da hukuncin kotun ba. Tawagar mu ta samu hujjojin kura-kurai a zaben, wanda muka yi imanin ya yi tasiri matuka kan sakamakon karshe.”
Ya sha alwashin ba zai huta ba har sai an yi adalci.
Gwamna Kefas da mataimakinsa Sanata Haruna Manu sun gayyaci Yahaya da jam’iyyar NNPP da su amince da hukuncin da kotun zabe ta yanke domin ceto dukiyar jihar, inda suka bukaci ’yan takarar da suka yi takara da su da su hada karfi da karfe domin cigaban jihar.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Wanda Zai Maye Gurbin El’Rufa’i a Matsayin Minista Ya Suma a Lokacin Tantance Shi
Wanda zai wakilci Kaduna a matsayin minista, Abbas Balarabe, ya fadi kasa wanwar yayin tantance shi a gaban majalisar dattawa
Yana gab da zama minista ya fadi kasa bayan gama gabatar da jawabinsa ga ‘yan majalisar
An zabi Balarabe ne a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
Wanda zai wakilci Kaduna a matsayin minista, Abbas Balarabe, ya fadi kasa wanwar yayin tantance shi a gaban majalisar dattawa.
Balarabe ya gama gabatar da jawabinsa ga ‘yan majalisar ya fadi yayin da daya daga cikin Sanatocin Kaduna ke yabonsa.