- Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar NIS Misis Wura-Ola Adepoju, ta bayyana cewa har yanzu masu neman takardun fasfo 112,351 ba su karba ba
- NIS ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu an karbi litattafan fasfo guda 91,981
- NIS ta bukaci masu nema su ziyarci wuraren da suke nema domin karbar takardun tafiye tafiye na Fasfo
Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Misis Wura-Ola Adepoju, ta bayyana cewa har yanzu masu neman takardun fasfo 112,351 ba su karba ba a fadin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja.
A halin da ake ciki, NIS ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu an karbi litattafan fasfo guda 91,981.
KARANTA WANNAN: PDP Tayi Rashin Babbar Jigo Ya Yin Da ta Fice Daga Jam’iyyar
Adepoju, wanda ta bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai a hedkwatar hukumar da ke Abuja, ta kara da cewa wannan adadin ya kasance har ya zuwa ranar 5 ga watan Oktoba.
Ta bayyana cewa ma’aikatar ta share dukkan takardun fasfo 204,332 bayan wa’adin makonni biyu da Ministan cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya bayar na hidimar a watan jiya.
Shugaban NIS ta bukaci masu bukatar su ziyarci wuraren da suke nema domin karbar takardun tafiye tafiye na Fasfo.
A wani labarin kuma, Ba Za a Amince da Yawan Mace-Macen Mata Masu Juna Biyu Ba a Najeriya – MRHC
Kungiyar Binciken Lafiyar Mata da Haihuwa, MRHC, ta koka da mace-macen mata masu juna biyu a kasar
Don magance matsalolin ana bukatar taimakon kowa da kowa, Yana da mahimmanci a kula da ceton rayukan mata masu juna biyu
Hakan ya sanya kirkiro wani shiri na wanda zai magance matsalar lafiyar mata
Kungiyar Binciken Lafiyar Mata da Haihuwa, MRHC, a ranar Alhamis, ta koka da mace-macen mata masu juna biyu a kasar, inda ta ce ba za a amince da shi ba.
MRHC, wacce ta bayyana cewa kashi 30 cikin 100 na mata suna mutuwa sakamakon juna biyu ko kuma abubuwan da suka shafi haihuwa, ta ce ta kirkiro wani shiri na tsawon wata guda wanda zai magance matsalar lafiyar mata a kasar.