- Rundunar ‘yan sandan a ranar Juma’a, ta gurfanar da wasu mutane shida a gaban wata kotun Majistare ta Ojo da ke jihar Legas
- Ana zargin masu laifin sun aikata mummunar barna kan kayan da suka sace
- Tuni suke fuskantar tuhuma kan wannan aika-aika
Rundunar ‘yan sandan a ranar Juma’a, ta gurfanar da wasu mutane shida a gaban wata kotun Majistare ta Ojo da ke jihar Legas bisa zargin su da kutsawa cikin wani gida da nufin yin sata.
Wadanda ake tuhumar su ne Salisu Musa mai shekaru 36; Awolu Isa mai shekaru 48; Sani Ibrahim dan shekara 28; Suraju Yunusa, 36; Habibu Yunus 28 da Usman Musa mai shekaru 28.
KARANTA WANNAN: Zaben Gwamna: Tinubu Zai Kaddamar da Gangamin Yakin Neman Zaben APC Ranar Lahadi
Mutanen shida sun gurfana gaban kotu a gaban Alkali L.K.J Layeni, bisa tuhume-tuhume biyar da suka hada da sata.
Sai dai kowannen su ya ki amsa laifin da ake tuhumar su da shi.
Dan sanda mai shigar da kara, Simon Uche, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne don aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Satumba a unguwar Abule Osun da ke Ojo, Legas.
Uche ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar da sauran wadanda ake zargin sun kutsa cikin harabar gidan mai kara mai suna Chigbo Udezuruigbo domin yin sata.
Ya bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun lalata wata na’urar hako mai dauke da abubuwa da dama, tare da sace kayanta.
Ya kara da cewa sassan na’urar sun kai kimanin Naira miliyan 5.5.
Laifin, ya ce ya sabawa tanadin sashe na 287 da 411 na dokar laifuka ta jihar Legas, ta shekarar 2015.
Layeni ya bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi Naira 500,000 kowanne, tare da tsayayyu mutane biyu ga kowannensu.
Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 25 ga watan Oktoba domin shari’a.
NAN
A wani labarin kuma, LP ta Karyata Rahoton Cewa Shugabannin Kananan Hukumomi 21 Sun Sauya Sheka Zuwa APC
Jam’iyyar Labour a jihar Kogi ta karyata labarin da ke fitowa kan cewa shugabannin kananan hukumomi 21 sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC
Ba bu yadda za’ayi shugabannin kananan hukumomin guda 21 su sauya sheka zuwa APC sau uku
Jam’iyyar Labour ta mayar da hankali ne kan batutuwan da za su ceto mutanen jihar
Jam’iyyar Labour a jihar Kogi ta karyata labarin da ke fitowa kan cewa shugabannin kananan hukumomi 21 sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar Labour ta Jihar, Idakwo Emmanuel, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Lokoja ranar Juma’a.