- Majalisar dokokin jihar Kano ta gwangwaje Auwalu Salisu, direban babur mai kafa uku da Naira miliyan 1.5
- Hakan ya biyo bayan mayar da naira miliyan 15 ga mai shi daya manta a adaidaita sahun sa
- Tuni dai majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta dauki nauyin karatunsa har zuwa matakin jami’a
Majalisar dokokin jihar Kano ta karrama Auwalu Salisu, direban babur mai kafa uku da ya mayar da miliyan ₦15m ga mai shi, dan kasar Chadi, wanda ya bar shi a cikin Keke Napep, da Naira miliyan 1.5, Tribune Online ta rahoto.
Sai dai a ranar Litinin, a zaman majalisar, Auwalu Salisu ya karbi kyautar Naira miliyan 1.5 daga ‘yan majalisar Kano.
KARANTA WANNAN: ‘Yan Sanda Sun Baje Kolin Wasu da Ake Zargi da Lalata Kayayyakin Gadar Neja Ta Biyu
Shugaban majalisar wanda ya jagoranci zaman majalisar ya ce mai girma Auwalu Salisu dan kasa ne wanda ya yi fice wajen ganin ya mayar da makudan kudaden da suka kai naira miliyan goma sha biyar.
Majalisar ta ba shi takardar yabo kuma kowane memba ya ba da kudi Naira miliyan 25 yayin da majalisar ta ba da gudummawar Naira 500,000 da ya kai Naira miliyan 1.5.
Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta dauki nauyin karatunsa har zuwa matakin jami’a.
Da yake jawabi bayan bayar da tallafin, matukin baburdin Dan Baba ya nuna jin dadinsa ga ‘yan majalisar bisa wannan karimcin.
Ya kara da cewa ba za a manta da wannan karimcin nasu ba, ya kuma yi addu’ar samun nasara a zaman tattaunawa a majalisar.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade a Gwamnatinsa Bayanai Sun Fito
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ya amince wasu mutane hudu a matsayin mambobin tawagar masu ba shugaban kasa shawara
Shugaban ya bukaci dukkan sabbin masu rike da mukaman da su kasance masu bin ka’idoji da ladabi wajen gudanar da ayyykan su
Wadanda aka nada sun kasance kwararru ta fanni daban-daban
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ya amince da nadin Fela Durotoye da wasu mutane hudu a matsayin mambobin tawagar masu ba shugaban kasa shawara.
An nada Durotoye a matsayin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Ƙimar Ƙasa da kuma Adalci ga Jama’a.