- Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da mayar da kwalejin koyan larabci ta zuwa wata cibiya ta musamman ta koyar da ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci
- Sabuwar cibiyar za a gudanar da ita ne tare da hadin gwiwar jami’ar Al-Azhar kuma za ta samar da daliban da za su dinga wa’azi da zai dakile akidar Boko Haram
- Gwamnan ya umurci sabuwar hukumar ilimin Larabci da Tsangaya da ta karbi ragamar tafiyar da dukkanin makarantun Tsangaya da na islamiyya a jihar
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da mayar da kwalejin koyan larabci ta Mustapha Umar Elkanemi da ke Maiduguri zuwa wata cibiya ta musamman ta koyar da ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci da nufin dakile akidar Boko Haram.
Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafofin yada labarai, Isa Gusau ya fitar, ya bayyana hakan a ranar Talata a lokacin da ya kai ziyarar duba kwalejin, domin shirye-shiryen sauya sheka.
KARANTA WANNAN: Tallafi: Najeriya Ta Shigo da Lita Biliyan 23.5 Na PMS a Shekarar 2022 – NMDPRA
A cewar sanarwar, shirin na nufin mayar da martani ne ga barazanar kungiyar Boko Haram, wadda ta yi fice wajen fafutukar yaki da ilimi da yada tsatstsauran ra’ayi da batanci ga addinin musulunci.
Sanarwar ta ce idan aka kafa sabuwar cibiyar za a gudanar da ita ne tare da hadin gwiwar jami’ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira ta kasar Masar kuma za ta samar da daliban da za su koma kananan hukumomin jihar Borno 27 domin yin wa’azi da zai dakile akidar Boko Haram.
Gwamna Zulum ya sanar da cewa, “Mun zo nan ne domin yin nazari kan karfin wannan makaranta, ta fuskar aikin dan adam da kayayyakin more rayuwa da nufin mayar da ita cibiyar Al-Azhar”.
A halin da ake ciki Gwamna Zulum ya umurci sabuwar hukumar ilimin Larabci da Tsangaya da aka kafa ta jihar Borno da ta karbi ragamar tafiyar da dukkanin makarantun Tsangaya da na islamiyya a jihar Borno.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Kotun Sojoji Ta Yankewa Manjo Janar Hukuncin Daurin a Gidan Yari
Wata kotun sojin Najeriya ta musamman ta yanke wa tsohon Manajan Darakta na rukunin, Nigerian Army Properties Limited, Manjo Janar Umaru Mohammed, hukuncin daurin shekaru 7
Biyo bayan yanke hukuncin kotun ta umarce shi da ya mayar da wasu makudan kudade na dala da kuma Naira
Duk da ya ki amsa dukkan zarge-zargen, amma kotun ta same shi da wasu laifuka
Wata kotun sojin Najeriya ta musamman da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta yanke wa tsohon Manajan Darakta na rukunin, Nigerian Army Properties Limited, Manjo Janar Umaru Mohammed, hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.
Kotun ta kuma umarce shi da ya mayar da dala 2,178,900 da kuma Naira biliyan N1.65bn ga kadarorin Sojoji da NAPL.