- Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isa-Sabon dake jihar Sokoto, Abdulkadii Jelani Danbuga ya rasu
- Dan majalisar kafin rasuwarsa ya yi fama da rashin lafiya na wani lokaci
- Za’a yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a yau laraba
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isa-Sabon a jihar Sokoto, Abdulkadii Jelani Danbuga ya rasu, Tribune Online ta rahoto.
Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar wanda ya zanta da wakilinmu bisa sharadin sakaya sunansa ya ce gawarsa za ta isa Sokoto a yau Laraba domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
KARANTA WANNAN: Ka Fadawa ’Yan Najeriya Wanene Kai, Obi Ya Gaya Wa Shugaba Tinubu
Ya bayyana cewa dan majalisar wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar APC mai mulki ya rasu ne a ranar Talata da yamma a Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya na wani lokaci.
A wani labarin kuma, Zaben Gwamnan Bayelsa: Har Yanzu Sylva Ne Dan Takararmu – APC
Jam’iyyar APC ta bayyana cewa tana shirin ci gaba da kaddamar da yakin neman zaben gwamnan Bayelsa
Alkali ya yanke hukuncin cewa Sylva da aka rantsar da shi sau biyu a matsayin gwamna zai saba wa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya
APC tace PDP ta koma yin mu’amala da kalaman da basu dace ba don karkatar da hankali da haifar da rudani a tsakanin al’ummar jihar
Jam’iyyar APC ta bayyana cewa tana shirin ci gaba da kaddamar da yakin neman zaben gwamnan Bayelsa da za a yi a ranar 14 ga watan Oktoba duk da cewa dan takararta, Cif Timipre Sylva an yi watsi da shi.
JARIDAR DIMOKURADIYYA a baya ta rahoto cewa Mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, a wani hukunci da ta yanke a ranar Litinin, ta haramtawa Sylva shiga takara a zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwanba.