- Jami’an ‘yan sandan Kogi, sun cafke wani yaro Goodness Oshodi, dan shekara 19 bisa zargin binne kanensa mai suna Friday Oshhodi
- Mahaifiyar yaron ta umurci babban danta da ya hukunta wanda abin ya shafa saboda sace mata Naira dubu N10,000
- Kafin aiwatar da umurnin mahaifiyarsa wanda ake zargin ya fara lakadawa mai laifin dukan tsiya kafin ya yanke shawarar binne shi da ransa
Jami’an ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kogi, sun cafke Goodness Oshodi, wani yaro dan shekara 19, wanda ake zargin ya binne kanensa mai suna Friday Oshhodi da ransa bisa umarnin mahaifiyarsa kan satar Naira 10,000, Tribune Online ta rahoto.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a unguwar Apamisede, dake karamar hukumar Adavi ta jihar.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Kebbi Ta Amince Wa Gwamna Idris Karin Kasafin Kudin N19.8bn
Sai dai wanda abin ya shafa ya yi sa’a inda makwabta suka ceto shi daga halaka.
A cewar shaidun gani da ido, mahaifiyar yaron ta umurci babban danta da ya hukunta Friday saboda sace mata N10,000.
Babban ɗan’uwan da ke aiwatar da umurnin mahaifiyarsa ya fara dukan Friday kafin ya yanke shawarar binne shi da ransa.
Da yake magana kan dalilin da ya sa ya yanke shawarar binne dan’uwansa da rai, Goodness ya ce yana aiwatar da umarnin mahaifiyarsu ne kawai da ta bukaci ya hukunta dan uwansa saboda ya sace mata Naira N10,000 kuma ya yi kokarin gudu da ita kamar yadda ya saba.
A cewarsa, mahaifiyar sa wadda ta umarce shi da ya hukunta Friday, ta je coci lokacin da ya binne shi da rai.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Aya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama yaron kuma ana yi masa tambayoyi.
“Eh, muna sane. An kama yaron, ana ci gaba da gudanar da bincike kan dalilin da ya sa kuma ta yaya hakan zai iya faruwa,” inji shi.
A wani labarin kuma, Ku Kula da Lafiyar Kwakwalwarku, Uwargidan Shugaban Kasa Ta Bukaci ‘Yan Najeriya
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta bukaci ‘yan Najeriya da su ba da fifiko ga lafiyar kwakwalwa
Lafiyar kwakwalwa hakki ne na duniya baki daya’, ya kamata kowannenmu ya kara mai da hankali kan lafiyar kwakwalwarmu da ma sauran mutane
Ya kamata ‘yan Najeriya su taimaka wa matasa su shawo kan kalubalen tunaninsu da inganta alaka mai kyau
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta bukaci ‘yan Najeriya da su ba da fifiko ga lafiyar kwakwalwa a cikin matsin lambar da al’umma ke fuskanta da kalubalen da ake fuskanta a shafukan sada zumunta.
Uwargidan Tinubu ta bayyana hakan ne ta wani sako da ta wallafa a shafinta na X (tsohon shafin Tuwita) a ranar Talata domin tunawa da ranar kiwon lafiyar kwakwalwa ta duniya ta 2023.