- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya shawarci ma’aurata 1,800 su guji yunƙurin duba wayoyin abokan zaman su
- Bincika wayar abokin zaman aure na daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa mutuwar aure
- Ku zauna lafiya tare da kasancewa masu hakuri da juna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya shawarci ma’aurata 1,800 da aka daura musu aure da su guji yin yunƙurin duba wayoyin abokan aure domin gujewa duk wani abu da zai iya haifar da lalacewar aurensu.
Wannan nasihar ta zo ne a yayin wata liyafar da gwamnatin jihar ta shirya wa ma’auratan a gidan gwamnati, kamar yadda babban kwamandan hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana.
KARANTA WANNAN: EPL: Sarkin Qatar Ya Janye Daga Takarar Sayen Man Utd
Yace daga cikin ma’aurata 1,800 an dakatar da daurin auren mutane 264 saboda wasu cututtuka, kuma a halin yanzu wadannan ma’auratan suna jinya.
Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa duba wayar abokin aure na daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rugujewar aure a kasar nan.
Ya shawarci ma’auratan da su guji ayyukan da za su iya haifar da rikici a tsakaninsu, inda ya jaddada cewa sun riga sun samu nasiha sosai daga bangarori daban-daban da suka hada da malaman addini, iyaye, ‘yan uwa da sauran su kan yadda za su zauna lafiya da juna.
A cewarsa, “Duba wayar abokin aure da ma’auratan ke yi na daya daga cikin abubuwan da ke kawo rabuwar aure a kasar nan, inda ya shawarce su da su guji duk wani abu da zai kawo rikici a tsakaninsu.”
Ya ce, “An yi muku nasiha da kowa da kowa. Na yi imani an yi muku nasiha sau dubu. Malamai da iyaye da ’yan uwa da ma ’yan kasuwa sun yi muku nasiha kan yadda za ku zauna lafiya da juna.
Don haka ya kara da cewa “Amma, ina da shawara guda daya a gare ku. Wato duba wayoyin mazaje sannan Karka leko wayar matarka domin wannan shine babban dalilin rabuwar aure.
Kwankwaso ya ci gaba da cewa gwamnan jihar Kano mai ci Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da gudanar da ayyukan da suka gada tare da gabatar da ayyuka bisa tsarin da ya dace. Ya yi kira ga al’ummar Kano da su marawa gwamnatinsa baya.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa, an zabo wadanda suka ci gajiyar daurin auren ne daga dukkan kananan hukumomi 44 da kuma mazabu 484 na jihar, inda aka zabo akalla ma’aurata 30 daga kowace karamar hukuma.
Gwamnati ta bayar da tallafin daurin auren da suka hada da sadaki, kayan daki, kayan abinci na aure, da kuma tallafin Naira 20,000 ga matan aure don fara kananan sana’o’i a gidajen aurensu.
Ya bukaci ma’auratan su zauna lafiya kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Kare Kan Iyakokin Kasa
Ministan harkokin cikin gida Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa wani kwamiti mai mutane 13 da zai tantance bukatu a kan iyakokin kasa
Ministan ya tuhumi kwamitin da ya samar da wani shiri na tabbatar da tsaron iyakokin Najeriya yadda ya kamata
Aa umurci kwamitin ya yi kokarin yin tsayuwar daja tare da samar da tsarin kula da iyakokin da za a iya aiwatarwa don tabbatar da tsaron kasa
Ministan harkokin cikin gida Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa wani kwamiti mai mutane 13 da zai gudanar da tantance bukatu a kan iyakokin kasar.
Mambobin kwamitin sun fito ne daga jami’an ma’aikatar; Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, Jami’an Tsaron Farin Kaya na Najeriya, Hukumar kashe gobara ta Tarayya, Hukumar Raya Al’umma ta Kan iyaka, Hukumar Kula da Iyakoki, da kuma masu ba da shawara.