- Gwamnatin Kano ta ce ta kashe Naira biliyan 1.3 wajen biyan kudin rijistar jarabawar dalibai marasa galihu na jihar su kimanin 57,000
- Gwamnati ta ba da fifiko wajen samar da kayayyakin koyo na zamani ga makarantun gwamnati a jihar
- An bukaci ma’aikatan gwamnati da su tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukansu saboda gwamnati ba za ta lamunci cin hanci da rashawa da wawure dukiyar kasa ba
Gwamnatin Kano ta ce ta kashe Naira biliyan 1.3 wajen biyan kudin rijistar dalibai marasa galihu na jihar su kimanin 57,000 ga hukumar shirya jarabawar ta kasa da hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa.
Gwamna Abba Kabir-Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake kaddamar da rabon kayayyakin ilimi sama da miliyan biyu ga makarantun matakin farko.
KARANTA WANNAN: Gwamna Sani Ya Yi Nada Sabon Nadi a Gwamnatinsa Bayanai Sun Fito
Ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen samar da kayayyakin koyo na zamani ga makarantun gwamnati a jihar.
“Lokacin da daliban ke daukar darusa a kan daben siminti ba komai ya kare a jiharmu. Tuni, muna da tsari don tabbatar da samar da kayan daki ga cibiyoyin makarantun gwamnati.
“Muna gudanar da gwamnatin da ta dace da za ta tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga daliban mu,” in ji Yusuf.
Ya sanar da cewa gwamnatin jihar na gina sabbin makarantun mata da maza guda 130 a wani yunkuri na daukar yaran da ba su zuwa makaranta a shekara guda mai zuwa.
Ya kuma bayyana cewa jihar na biyan N20,000 duk wata ga ‘yan mata marasa galihu guda 40,000 ‘yan asalin jijar domin karfafa masu karatu, rikewa da kuma kammala makarantu. Yayin da mambobi 5,000 na Kungiyar Bayar da Sabis na Ilimi na Jiha za a dauke su aikin gwamnati.
“Na umurci kwamitin da aka kafa ya tantance mambobin kungiyar bayar da hidimar ilimi da su gabatar da sunayensu da cancantar aikin gwamnati cikin gaggawa,” inji shi.
Gwamnan ya shawarci ma’aikatan gwamnati da su tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukansu, yana mai gargadin cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci cin hanci da rashawa da wawure dukiyar kasa ba.
Tun da farko a nasa jawabin, Kwamishinan Ilimi Umar Haruna-Doguwa, ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na inganta samar da ingantaccen ilimi kyauta ga kowa da kowa ta hanyar samar da kayayyakin koyo ga makarantun da ke fadin kananan hukumomi 44.
A wani labarin kuma,‘Kadawo Ofis Ko Ya Yi Murabus’ – PDP Ta Ba Gwamnan APC Wa’adin Wasu Kwanaki
Jam’iyyar PDP a jihar Ondo ta bai wa Gwamna Oluwarotimi Akeredolu wa’adin kwanaki uku ko dai ya koma ofishin gwamna ko kuma ya yi murabus
Ba a ga gwamnan a jihar ba tun bayan dawowarsa daga jinya a kasar waje sama da makonni hudu da suka gabata
Dole ne Gwamna ya koma bakin aikinsa. Ba zai iya jurewa yin mulkin mu ta wakilci ba
Jam’iyyar PDP a jihar Ondo ta bai wa Gwamna Oluwarotimi Akeredolu wa’adin kwanaki uku ko dai ya koma ofishin gwamna da ke Akure, ko kuma ya yi murabus.
Kungiyar matasan jam’iyyar ta fitar da wa’adin ne a ranar Litinin a sakatariyar jam’iyyar da ke Akure, babban birnin jihar Ondo, yayin da suke nuna rashin amincewa da ci gaba da rashin halartar gwamnan.