- Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya caccaki mutanen da ke yada jita-jitar komawar sa kasar Jamus domin jinya
- Gwamnan ya bayyana cewa labarin ba gaskiya bane kuma ba shi da tushe balle makama
- Wannan jita-jitar na daya daga cikin dabarun da wasu ‘yan siyasa ke amfani da ita wajen tunzura jama’a kan gwamnan
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, a ranar Talata ya caccaki mutanen da ke yada jita-jitar komawar sa kasar Jamus domin jinya a matsayin mugaye, da rashin kunya, da mayaudara, inda ya bayyana cewa suna yunkurin haddasa fargaba a jihar.
KARANTA WANNAN: An Yi Ram da Wani Mutum da Ake Zargi Da Damfarar Masu Neman Aiki
Akeredolu, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaransa, Mista Richard Olatunde, ya bayyana cewa labarin ba gaskiya bane kawai amma ba shi da tushe.
Ya kara da cewa wannan jita-jitar na daya daga cikin dabarun da wasu ‘yan siyasa ke amfani da ita wajen tunzura jama’a kan gwamnan.
A cewar Olatunde, wasu ’yan siyasa ne da suka nutse suka shirya labarin kuma har yanzu suna jin radadin rashin tsammani.
Ya kuma yi gargadin a guji yada labaran karya sannan ya bayyana cewa gwamnan bai taba shirin komawa kasar Jamus don jinya ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Rahoton da aka yi na cewa gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, na shirin komawa Jamus don hutun jinya, muguya ne kuma yaudara ce.
“Yan siyasa ne masu nutsewa suka tattara rahoton kuma har yanzu suna jin zafin rashin tsammani.
“Yayin da mutanen jihar ke farin ciki da dawowar gwamnan lafiya daga hutun jinya, wadannan ‘yan siyasar da ke cikin rudani sun kasance cikin dare ba su yi barci ba, suna cizon hakora saboda nadamar rashin nasarar shirin da suka yi.”
Ya ci gaba da cewa, “Labarin da ake ta yadawa ba shi da tushe ballantana makama, kuma kawai hasashe ne na tunanin miyagun ‘yan siyasa.
“A gare mu, mun himmatu wajen magance matsalolin da jama’ar jihar ke da shi na gaske. Wannan ne ya sa aka ba da fifikon ci gaba a karkashin gwamnatin Akeredolu.
“Gwamnati ba ta batun showbiz ba ne, inda gwamna ya fara faretin kaya a dandalin kasuwa don sanar da kasancewarsa a jihar.
Mun fahimci mahimmancin ci gaba a matsayin babban jagoran zaman lafiya, ci gaba, da daidaito tsakanin al’umma.
Gwamnatin Gwamna Akeredolu Ta Ci Gaba Da Nuna Himma Ga Ci Gaban Jihar.
Kwanan nan, ya amince da daukar kwararrun likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya a matsayin nunin jajircewarmu na inganta tsarin kiwon lafiyar jihar.
“Gwamnan ya kuma rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudin shekarar 2023 na hukumar bunkasa albarkatun man fetur ta jihar Ondo (OSOPADEC) ya zama doka, bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da shi.
“Wannan wani muhimmin mataki ne na ciyar da yankin da ake hako mai.”
“Bugu da ƙari, muna alfahari da bayar da rahoton cewa ana ci gaba da aiki cikin sauri a kan aikin gina asibitin koyarwa na Jami’ar Kimiya mai gadaje 250 a Akure da Garin Ondo.
Haka kuma ana ci gaba da aikin gina gadar sama ta Akure dake mahadar Onyarubulem/Shagari, kuma muna samun ci gaba.
“Don bunkasa samar da kudaden shiga, Gwamna Akeredolu ya amince da daukar sabbin ma’aikata 150 a ma’aikatar tattara kudaden shiga ta jihar.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Ganduje, ‘Yan Majalisar Dokokin Ondo Sun Shiga Ganawar Sirri Kan Wani Muhimmin Batu
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, yana ganawa da tawagar ‘yan majalisar dokokin Ondo da suka fusata domin sasanta rikicin da ake shirin tsige mataimakin gwamnan jihar
Cigaban dai na zuwa ne kwanaki takwas bayan da shugaban APC na Kasa ya kafa kwamitin da zai sasanta rikicin siyasar jihar
Tawagar ta isa sakatariyar jam’iyyar APC ta kasacikin wani katafaren ayari, tare da rakiyar jami’an tsaro
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yana ganawa a yanzu haka da tawagar ‘yan majalisar dokokin jihar Ondo da suka fusata da kuma ‘yan kwamitin sulhu da aka kafa domin sasanta rikicin da ake shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Ayiedatiwa.
Tawagar wacce ta isa sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da misalin karfe 1.25 na rana a cikin wani katon ayari, tare da rakiyar jami’an tsaro masu tsauri.