- Ministan bunkasa ma’adanai na kasa, Dele Alake, ya bada sharudda ga kamfanonin hakar ma’adinai na kasa da kasa
- Dole kamfanonin su sanya hannun jari wajen sarrafa kayayyaki a cikin gida domin samun lasisi
- Ministan ya bayyana hakan ne a yayin taron makon ma’adinan Najeriya
Ministan bunkasa ma’adanai na kasa, Dele Alake, ya bada sharudda ga kamfanonin hakar ma’adinai na kasa da kasa da ke neman lasisin yin aiki a Najeriya.
A cewarsa, za a bukaci irin wadannan kamfanoni su sanya hannun jari wajen sarrafa kayayyaki a cikin gida domin samun lasisi.
KARANTA WANNAN: FCTA ta Dage Haramcin Amincewar Yin Gine-Gine
Alake ya bayyana hakan ne a yayin taron makon ma’adinan Najeriya da ke gudana a Abuja.
Ya lura cewa, kamfanonin hakar ma’adinai suna buƙatar gabatar da tsare-tsaren kasuwanci don “ƙara darajar” kafin a ba su lasisi kuma manufar ta kasance ta hanyar samar da ayyukan yi.
A cikin kalamansa.
“Na yi farin cikin ambata cewa irin wannan shirin ya riga ya fara aiki, saboda tuni wasu kamfanoni suka fara aiki a Najeriya.”
Ministan ya bada misali da wani kamfani na kasar Sin mai suna Ganfeng Lithium Industry Ltd wanda a halin yanzu yake gina kamfanin sarrafa lithium na dalar Amurka miliyan 250 a jihar Nasarawa a matsayin babban misali na irin jarin da gwamnati ke nema.
Ana sa ran ginin zai sarrafa kusan tan 18,000 na ma’adinan lithium a kullum don samar da batura da aka kera don motocin lantarki, kamar yadda ministan ya bayyana.
Alake ya ce ana sabunta sana’ar hakar ma’adanai ta zamani, kuma gwamnati na saka hannun jari wajen tattara bayanai, inda ta kashe sama da Naira biliyan 15 a tsawon shekaru bakwai wajen samar da bayanan ma’adanai ta hanyar National Integrated Mineral Exploration Project (NIMEP).”
A wani labarin kuma,‘A Tsinke Igiyar Auren Dake Tsakanina da Mijina’ – Jami’ar ‘Yar Sanda Ta Roki Kotu
Wata jami’ar ‘yar sanda, Angela Adams, ta roki wata kotun kwastomari ta raba auren da ke tsakaninta da mijinta, Titus
Mijina ya karbi rancen tsabar kudi har Naira N750k da sunana daga wani banki
Kamar wata yarinya a duk lokacin da muka sami ɗan rashin fahimta mijina yana lakadamun dukan tsiya
Wata jami’ar ‘yar sanda, Angela Adams, ta roki wata kotun kwastomari da ke zamanta a Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata da ta raba auren da ke tsakaninta da mijinta, Titus, kan rikicin cikin gida.
Sa’ad da ake ci gaba da shari’ar ƙarar auren da ta kai mijinta kotu, ta ce: “Mijina yakan yi min dukan tsiya a duk lokacin da muka sami ɗan rashin fahimta. Yakan buge ni kamar yaro.