- Majalisar dattawa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar EFCC
- Kasancewar Olukoyede a matsayin sabon shugaban EFCC na zuwa ne bayan dakatar da tsohon shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa
- Tabbatar da mutanen biyu ya biyo bayan kimanin mako guda bayan da shugaba Bola Tinubu ya nada su
Majalisar dattawa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Sannan ta kuma tabbatar da nadin Muhammad Hammajoda a matsayin sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
KARANTA WANNAN: VIO Ne Kawai Ke da Ikon Yin Bincike, Bayar da Rahotannin Hatsari – Jami’i
JARIDAR DIMOKURADIYYA a baya ta rahoto cewa Olukoyede ya kasance a Majalisar Dokoki ta Kasa tare da wasu Ma’aikatan Gudanarwa na Hukumar.
Tabbatar da mutanen biyu ya biyo bayan tantance su ne da babban zauren majalisar ya yi a ranar Laraba da yamma, kimanin mako guda bayan da shugaba Bola Tinubu ya nada su.
Nadin na su ya kasance na tsawon shekaru hudu.
Zaton Olukoyede a matsayin sabon shugaban EFCC na zuwa ne kusan watanni hudu bayan Tinubu ya dakatar da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Mista Abdulrasheed Bawa.
A wani labarin kuma, Rundunar ‘Yan Sanda ta Kame Mutane 298 da Ake Zargi da Aikata Mabambanta Laifuka
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta yi ram da kimanin mutane 298 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban
An samu riba mai yawa a rigakafin yaki da laifuka da rundunar ta dauka a ci da duk wani nau’i na miyagun laifuka a jihar
Masu laifin da aka cafke sun kware wajen aikata laifukan da ake zargin su da aikatawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta yi ram da kimanin mutane 298 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin kwata na uku na shekarar 2023.
Wata sanarwa da DSP Lawan Shiisu, kakakin rundunar ‘yan sandan ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa ‘yan sandan sun kwato bindigogi da dabbobi 64 na sata a lokacin nazarin.