- Chelsea ta bayyana cewa ‘yan wasanta biyu Carney Chukwuemeka da Trevoh Chalobah ba za su buga wasan da Arsenal za ta yi ba
- Hakan ya biyo bayan murmurewa daga raunukan da suka samu
- ‘Yan wasan dai basu buga wasanni da dama ba a wannan kakar
Chelsea ta bayyana cewa Carney Chukwuemeka da Trevoh Chalobah ba za su buga wasan da Arsenal za ta yi a gasar Premier ba a ranar Asabar din nan.
‘Yan wasan biyu dai sun samu koma baya wajen murmurewa daga raunukan da suka samu.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Duba Dokar EFCC – Akpabio
“Dan wasan baya Trevoh Chalobah da dan wasan tsakiya Carney Chukwuemeka duk sun fuskanci koma baya a yunkurinsu na dawowa daga raunin da suka samu a farkon kakar wasa ta bana.
Sanarwar da kulob din ya fitar ta ce “Yanzu za a sake duba su kafin su ci gaba da gyare-gyare a Cobham tare da ma’aikatan lafiya na kulob din.”
Chukwuemeka bai buga wa Blues wasa ba tun lokacin da ya ji rauni a gwiwarsa a karawar da suka yi da West Ham.
Shi kuwa Chalobah bai buga wasa kwata-kwata a wannan kakar ba, kuma har yanzu yana murmurewa daga raunin da ya samu a cinyarsa.
A wani labarin kuma, Gwamna Akeredolu Zai Iya Yin Mulki Daga Kowane Yanki Na Najeriya – Lauya
Wani lauya mai kare hakkin bil’adama Morakinyo Ogele ya bayar da hujjar cewa Gwamna Akeredolu na Ondo zai iya gudanar da mulkin jihar daga kowane bangare na cikin Najeriya
Lauyan yace rashin gwamna Akeredolu bai shafi mulkin jihar ta kowace fuska ba
Rashin zuwan gwamnan cikin jihar ya haifar da cece-kuce daga bangarori daban-daban yayin da ake ta nuna adawa da zaman gwamnan a wata jihar
Wani lauya mai kare hakkin bil’adama mazaunin Akure, Morakinyo Ogele, a ranar Laraba ya bayar da hujjar cewa Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo zai iya gudanar da mulkin jihar daga kowane bangare na cikin Najeriya.
Ogele ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Akure, babban birnin jihar Ondo.