- Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya sa ido a kan rabon tsabar kudi, abinci, da kayayyaki Naira miliyan 125 ga iyalai sama da 40k
- Kowane magidanci da rikici ya shafa zai amfana da wannan tallafin
- Gwamnan ya kaddamar da rabon kayayyakin tallafin don rage radadin cire tallafin man fetir ne a watan Yuli
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sa ido a kan rabon tsabar kudi, abinci, da kayayyaki Naira miliyan 125 ga iyalai sama da 40,000 a karamar hukumar Konduga a wani ci gaba da tallafin rage radadi.
Da yake jawabi a garin Konduga a ranar Alhamis yayin da ake gudanar da aikin raba kayayyakin, wanda ya gudana a cibiyoyi uku (3), Zulum ya bayyana cewa tallafin na da nufin rage wahalhalun da mazauna yankin ke fuskanta sakamakon cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi a watan Mayun bana.
KARANTA WANNAN: Gwamna Mutfwang Ya Sabbin Nade-Naden Mukamai Bayanai Sun Fito
Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da magidanta maza 15,000, inda kowannen su ya karbi buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da kuma buhun wake 10. Bugu da kari, mata 25,000 sun karbi tsabar kudi N5,000.
Zulum ya bayyana cewa, “A ci gaba da kokarin da muke na raba kayan agaji ga marasa galihu a jihar Borno, muna nan a Konduga. A cikin rabon na yau, kimanin mata 25,000 marasa galihu kowacce ta samu tallafi na Naira 5,000, wanda ya kai kusan Naira miliyan 125.
Baya ga wannan, mun kuma raba buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da wake buhu 10 kowanne ga magidanta 15,000.”
Zulum ya kaddamar da rabon kayayyakin tallafin don rage radadin cire tallafin man fetir ne a watan Yuli, inda aka fara rabawa kimanin gidaje 300,000 a fadin jihar Borno, inda aka baiwa al’ummomin da rikicin ya fi shafa.
Daga baya aka fadada rabon zuwa gidaje 400,000.
A kowace mazaba 27 da ke birnin Maiduguri da karamar hukumar Jere, sama da iyalai marasa galihu 2,000 ne suka amfana daga kokarin da Zulum ke yi.
Bugu da ƙari, kowane magidanci a yankunan karkara da tashin hankali ya shafa zai amfana.
Baya ga rabon kayan abinci, Zulum ya gabatar da wasu matakai da suka hada da samar da motocin bas guda 80 na jigilar manoma zuwa gonakinsu kyauta, motocin bas 30 na tallafin sufurin ma’aikatan gwamnati da ke zuwa ofisoshinsu, da samar da tallafin motocin bas na birni.
A wani labarin kuma, Kotun Allah Ya Isa Ta Tsayar da Ranar Sauraron Karar da Atiku Ya Shigar Kan Tinubu
Kotun Allah ya isa ta tsayar da ranar da za a saurari karar Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023
Hakan ya biyo bayan da alkalin kotun ya yi watsi da karar da Atiku da takwaransa na jam’iyyar LP Obi suka shigar saboda rashin cancanta
Tuni Atiku ya jajirce kan bayanan karatun Tinubu inda yace ya na cike da sabani da jabun takardu inda ya nemi kotun kolin ta kore shi daga mukaminsa
Kotun koli ta tsayar da ranar da za a saurari karar Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023, kan zaben shugaban kasa Bola Tinubu.
A cewar wata takarda da Jaridar Vanguard ta samu, kotun kolin ta sanya ranar Litinin 23 ga watan Oktoba domin sauraron karar.