- Hukumar EFCC ta samu hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso kan wani Sadiq Mustapha bisa zarginsa da laifin zambar fili
- An samu wanda ake zargin ne da laifin damfarar wani wani fili da kudin sa ya kai Naira miliyan 3.9
- Tuni alkali ya samu wanda ake zargi da aikata laifin zambar
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta shiyyar Maiduguri ta samu hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso kan wani Sadiq Mustapha bisa zarginsa da laifin zambar fili.
An samu Mustapha ne da laifin damfarar wani Yawudi Zarma kudi har Naira miliyan 3.9, bayan da (Zarma) ya biya kudin sayan fili da ya ce mallakin Mustapha ne.
KARANTA WANNAN: Tofa: Wani Abokin Hulda Ya Yi Yunkurin Banka Wa Banki Wuta
Filin yana nan ne a Layin Masana’antar Pompomari, Maiduguri dake babban birnin jihar Borno.
Mustapha dai bai kai wa mai siyan filin ba kuma bai mayar masa da kudinsa ba, kamar yadda rahoton ya nuna.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana hakan a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba.
Yayin da aka gurfanar da shi a gaban mai shari’a Umaru Fadawu na babbar kotun jihar Borno, Mustapha ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi kan zamba har ya zuwa adadin.
Dangane da rokonsa, lauyan masu shigar da kara, A. I Arogha, ya roki kotun da ta yankewa wanda ake kara hukuncin da ya dace.
Da yake yanke hukuncin, Fadawu ya yanke hukuncin daurin shekara guda a gidan yari tare da zabin tarar Naira N200,000.
A tuhume-tuhumen ya ce, “Kai Sadiq Mustapha a ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2017, ko a ranar 10 ga watan Agusta, a Maiduguri, da ke cikin sashin shari’a na wannan kotun mai girma, ka damfari Yawudi Zarma ya kai maka kudi naira miliyan uku da dubu dari tara, N3,900,000.00, akan cewa adadin da aka ambata yana wakiltar biyan kudin siyan fili mai lamba BO/2065/16, Plot No.7 on BOTP/64, dake Pompomari Industrial Layout a Maiduguri.
Tuhumar ta kara da cewa “Ka yi iƙirarin cewa shi ne mai shi kuma ta haka ne kuka aikata laifin da ya saba wa Sashe na 320 (a) na Dokar Shari’ar laifuka ta dokokin jihar Borno guda 102 kuma masu hukunci a karkashin sashe na 323 na wannan doka.”
A wani labarin kuma, Gobe Alhamis Babbar Kotun Nijeriya Zata Yanke Hukunci Akan Zaben Shugaban Kasa
A karshe dai kotun kolin ta sanya ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba domin yanke hukunci na karshe a kararraki biyu da suka rage na kalubalantar halascin ko akasin haka na ayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ya gabata.
Koke ne da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da takwaransa na jam’iyyar Labour, LP, Peter Gregory Obi suka shigar.