- Akalla mutane 20 ne suka jikkata sakamakon fashewar wata tankar mai a wani gidan mai da ke unguwar Rigasa a jihar Kaduna
- Motar dakon man ta tarwatse a lokacin da ta sauke mai ya yin da lamarin ya faru
- Sakaci ne ya jawo afkuwar lamarin daga bangaren ofishin da ke karbar man
Akalla mutane 20 ne suka jikkata sakamakon fashewar wata tankar mai a wani gidan mai da ke unguwar Rigasa a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna a ranar Laraba.
Wadanda lamarin ya rutsa da su da suka samu raunuka daban-daban daga lamarin sun hada da ‘yan kwana-kwana biyar, da ‘yan sintiri na jihar Kaduna, da kuma masu wucewa.
KARANTA WANNAN: Tinubu Shugaban Najeriya Ne, Ba ga APC Kadai Ba – Wike
Yanzu haka dai jami’an kashe gobara na samun kulawa a asibitin kwararru na Barau Dikko da ke Kaduna, kamar yadda daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Mista Paul Aboi ya bayyana a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa motar dakon mai tana sauke mai ne a lokacin da lamarin ya faru a ranar Laraba.
Ya dora alhakin lamarin a kan sakaci daga bangaren ofishin da ke karbar man, inda ya ce bai kamata a yi aikin sauke man da rana ba.
Ya kuma gargadi masu arzikin man fetur din da su guji jefa rayuwarsu cikin hadari ta hanyar sauke kayan a daidai lokacin da ya dace (da yamma).
A wani labarin kuma, Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio Ya Taya Tinubu Murna Kan Hukuncin Kotun Koli
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya taya shugaba Bola Tinubu murnar lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 da kotun koli ta tabbatar masa
Hukuncin da kotun kolin ta yanke ya warware lungu da sako na karshe a kan turbar zamantakewa da siyasa da shugaba Tinubu ya yi wa al’ummar kasar alkawari
Ina kira ga duk tsoffin abokan hamayyar siyasar shugaban kasa da su nuna kyakykyawan fahimta ta hanyar hada hannu da gwamnatin Bola Tinubu
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya taya shugaba Bola Tinubu murnar lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 da kotun koli ta tabbatar masa, yana mai bayyana hukuncin a matsayin wanda ya nuna ra’ayin jama’a.
Akpabio, a cikin sakon taya murna ga Tinubu, ya ce hukuncin da kotun kolin ta yanke, abin farin ciki ne, domin a karshe ya warware lungu da sako na karshe a kan turbar zamantakewa da siyasa da shugaba Tinubu ya yi wa al’ummar kasar alkawari.