- Hukumar ICPC ta shigar da kara a gaban kotu kan tsohon shugaban tsangayar shari’a ta jami’ar Calabar UNICAL, Farfesa Cyril Ndifon
- ICPC tare da hadin gwiwar hukumar DSS ta kama babban malamin da aka dakatar bayan ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa
- Ana zargin farfesan da laifin cin zarafi wata daliba
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran laifuka ICPC ta rawaito a ranar Litinin cewa ta shigar da kara a gaban kotu kan tsohon shugaban tsangayar shari’a ta jami’ar Calabar UNICAL, Farfesa Cyril Ndifon, Tribune Online ta rawaito.
Mai magana da yawun hukumar ta ICPC, Misis Azuka Ogugua, ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a Abuja, inda ta ce gurfanar da Ndifon kan tuhume-tuhume hudu ya biyo bayan kammala binciken da ICPC ta yi kan zargin Farfesan da aikata munanan dabi’u da ya yi wa wasu dalibansa.
KARANTA WANNAN: Wata Mata Ta Gurfana a Gaban Kotu Kan Badakalar Kudi Miliyan 6
Tuhume-tuhume hudu da ake tuhumar Ndifon mai lamba FHC/ABJ/CR/511/2023, ya mayar da hankali ne kan cin zarafi da cin hanci da rashawa a hukumance da kuma cin zarafin ofishin, sabanin sashe na 8, 18, da 19 na ayyukan cin hanci da rashawa da Sauran Dokokin Laifuffuka masu alaƙa,na shekarar 2000.
Kakakin ta bayyana cewa hukumar ta ICPC tare da hadin gwiwar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama babban malamin da aka dakatar a ranar 4 ga watan Oktoba a Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba, bayan ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa.
A cewarta, “Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya karanta: Cewa kai, Farfesa Cyril Osim Ndifon (m) tsakanin watan Yuni-Satumba, 2023, a Calabar, a cikin ikon wannan kotun mai daraja, kuma yayin da kake jami’in gwamnati da ake tuhuma da alhakin kai harin takardun shaida na ɗalibai kamar yadda suka dace da koyo da halayensu a matsayin abin da ake buƙata don samun first-class a fannin Shari’a da shiga Makarantar Shari’a ta Najeriya.
“Sannan ka yi amfani da ofishin ku da matsayin ku na shugaban tsangayar shari’a ta Jami’ar Calabar don gamsar da kanku ta hanyar neman Hotunan tsiraici da bidiyo daga wata Ms ABC (ba sunan gaskiya ba), dalibar Diploma ta Jami’ar Calabar ta shekara 2, ta hanyar tattaunawa ta WhatsApp ta lambar wayar ku 0803**** kuma ta haka ne ya aikata laifin da ya sabawa hukuncin da S.19 na Dokar Lamuni da Sauran Laifuffuka masu alaƙa, 2000.”
Har yanzu dai ba a kayyade ranar da za a gurfanar da Farfesa Ndifon a gaban kuliya ba.
A wani labarin kuma, EPL: Dalilin Da Yasa Man City Ta Ci Man Utd 3-0 – Ten Hag
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya mayar da martani kan rashin nasarar da suka yi a hannun Manchester City da ci 3-0
United tana matsayi na takwas a kan teburi, bayan da ta yi rashin nasara sau biyar a wasanni 10
Mun samu dama, amma ba mu amfani da ita ba kuma abin takaici ne
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya mayar da martani kan rashin nasarar da suka yi a hannun Manchester City da ci 3-0 a gasar Premier ranar Lahadi.
Erling Haaland ya zura kwallaye biyu a ragar Red Devils, yayin da Phil Foden shi ma ya zura kwallo a raga.