- Majalisar dattawa ta wanke tare da tabbatar da jerin sunayen kwamishinonin INEC goma da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada
- Shugaban Majalisar Dattawa shine wanda ya karanta wasikar ta Shugaba Tinubu na neman a tantance wadanda aka zaba
- Tuni majalisar ta wanke sabbin kwamishinon wadanda aka aike mata
Yanzu haka dai majalisar dattawa ta wanke tare da tabbatar da jerin sunayen kwamishinonin INEC goma da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada kuma ya aike wa majalisar.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta wasikar ta Shugaba Tinubu na neman a tantance wadanda aka zaba a zauren majalisar ranar Talata.
KARANTA WANNAN: Rashin Soyayya: Kotu Ta Raba Auren Shekara 6
Tinubu a cikin wasikar ya bayyana cewa matakin da ya dauka na neman a tantance wadanda ya nada ya yi daidai da tanadin sashe na 154 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, shekarar 1999 (kamar yadda aka gyara).
Wadanda aka tantance kuma aka tabbatar a ranar Laraba sun hada da, Mista Etekarnba Umoren (Akwa Ibom); Mr Isah Shaka Ehimeakne (Edo); Mrs Oluwatoyin Babalola (Ekiti); Abubakar Ahmed Ma’ali (Gombe) da kuma Shehu Wahab (Kwara).
Sauran sun hada da: Dakta Bunmi Omoseyin Babalola (Lagos), Aminu Kasimi Idris (Nasarawa), Mohammed Abubakar Sadiq (Niger), Dakta Anugbum Onioha (Rivers) da Abubakar Fawa Dambo (Zamfara).
Majalisar dattawan ta kuma tantance tare da tabbatar da Mista Shaakaa Chira a matsayin mai binciken kudi na tarayya.
Checks ya nuna cewa a watan Oktoban da ya gabata ne Tinubu ya nada Mista Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya don maye gurbinsa
Andrew Onwudili, wanda ya kasance mai kula da ofishin a matsayin mukaddashin.
A wani labarin kuma, Kungiyar Ma’aikatan Shari’a Ta Dakatar Shirin Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Gargadi
Kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta yi watsi da shirinta na ayyukan masana’antu da ta shirya gudanarwa
Sa’o’i kadan kafin fara yajin aikin, shugabannin JUSUN sun gana da masu ruwa da tsaki inda aka cimma matsaya
Rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron zai haifar da yajin aiki na dindindin ba tare da sanarwa ba
Kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta yi watsi da shirinta na ayyukan masana’antu da ta shirya gudanarwa a ranar 1 ga watan Nuwamba.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa kungiyar ta sanar da mambobinta da su ci gaba da yajin aikin sai baba-ta-gani idan har ba a biya su kashi 40 na alawus na musamman a karshen watan Nuwamba ba.