- Babbar kotun birnin tarayya ta bayar da umarnin a gaggauta sakin tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele ba tare da wani sharadi ba
- Alkalin kotun ya bayar da umarnin ne biyo bayan karar da Emefiele ya shigar
- Kotu ta umarci wadanda ake kara su gabatar da shi a gaban kotu a ranar da aka sanya don sauraren karar tare da yiwuwar kotu ta ba da belinsa
Babbar kotun birnin tarayya ta bayar da umarnin a gaggauta sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ba tare da wani sharadi ba, Daily Post ta rawaito.
Mai shari’a O.A. Adeniyi ya bayar da umarnin ne biyo bayan karar da Emefiele ya shigar.
KARANTA WANNAN: Ba Na Sha’awar Gudanar Da Mulkin Jihar Rivers – Wike
A cikin kudirin, tsohon gwamnan na CBN yana neman a sake shi daga hannun Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) har zuwa lokacin da za a saurare shi tare da tantance dalilin da ya sa ya samo asali.
Bayan sauraron karar, alkalin ya bayar da umarnin a saki Emefiele.
Emefiele ya bayyana sunan Tarayyar Najeriya, Babban Lauyan Tarayya (AGF), Shugaban Hukumar EFCC, da ita kanta EFCC a matsayin wadanda ake kara.
Kotun ta umarci masu kara na 3 da na 4 (Shugaban Zartaswa da EFCC) da su saki Emefiele daga tsaren shin da ake yi ba tare da wani sharadi ba.
“A madadin haka, an umarce su da su gabatar da shi a gaban kotu a ranar da aka sanya don sauraren karar da aka yi a kan sanarwar, tare da yiwuwar kotu ta ba da belinsa.
Kotun ta sanya ranar da za a ci gaba da sauraron karar a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023.
A wani labarin kuma, Tinubu Ya Bukaci A Gudanar da Zaben Gwamnoni Na Gaskiya da Adalci A Wasu Jihohi 3
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a gudanar da atisaye na gaskiya da adalci a zaben gwamna da za a yi a jihohin Imo da Bayelsa
Tinubu yayi wannan kirane a wajen baiwa ‘yan takarar Gwamna tuta a zaben da za’a yi a wasu jihohi uku
“Abin da nake roko a kai shi ne zabe na gaskiya da adalci Na yi imani za mu yi kyau
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a gudanar da atisaye na gaskiya da adalci a zaben gwamna da za a yi a jihohin Imo da Bayelsa a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a lokacin da ya gabatar da tutocin jam’iyyar ga ‘yan takarar jam’iyyar APC a jihohin da suka hada da Hope Uzodinma (Imo), Usman Ododo (Kogi), da Timipre Sylva (Bayelsa), a fadar shugaban kasa a Abuja.