- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya amince da hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ya tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu
- Obi yace kudurina na sabuwar Najeriya yana nan daram
- Dan takarar ta LP yace A watanni masu zuwa za mu gina jam’iyyar, za mu kara karfi, Za mu fito da karfi da himma ga sabuwar Najeriya
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya amince da hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ya tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu, The Nation ta rawaito.
Obi, ya ce hukuncin ba zai nuna karshen yunkurin Obidient ba.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Gwamnan Anambra Soludo Ya Yi Babban Rashi
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce da shari’a ta kare, yanzu jam’iyyar Labour tana adawa.
Ya ce kudurinsa na sabuwar Najeriya yana nan daram.
Obi ya fasa yin shiru kan hukuncin kotun koli a wani taron manema labarai a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba a Abuja.
Kotun koli a ranar 26 ga watan Satumba, ta amince da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke a ranar 6 ga Satumba, inda ta tabbatar da ayyana Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.
Kwamitin mai mutane bakwai karkashin jagorancin mai shari’a John Inyang-Okoro, ya yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu a zaben, da Obi wanda ya zo na uku ya shigar.
Obi ya ce: “A watanni masu zuwa za mu gina jam’iyyar, za mu kara karfi. Za mu gina wadannan matasa. Za mu fito da karfi da himma ga sabuwar Najeriya.
“Gaba yana da ƙarfi. Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne mu tabbatar da cewa mun yi abin da ya dace domin amfanin Nijeriya.”
A wani labarin kuma, Ana Fargabar Mutane 3 Sun Rasa Ransu Sakamakon Tashin Gobara a Ofishin Jakadancin Canada
Akalla mutane uku ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a Ofishin jakadancin Canada dake Abuja
Tuni bayan tashin gobarar aka kwashe ma’aikatan ofishin jakadancin zuwa mafaka da sauran wurare masu aminci
Gobarar ta tashi ne a lokacin da ake tsaka da gyaran tashar samar da wutar lantarki ta ofishin jakadancin
Akalla mutane uku ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a Ofishin jakadancin Canada da sanyin safiyar ranar Litinin a Abuja.
A cewar shaidar gani da ido, gobarar ta tashi ne a lokacin da ake gyaran tashar samar da wutar lantarki ta ofishin jakadancin, inda ta lakume tare da kashe mutane uku da ke cikin tawagar ma’aikatan, yayin da mutum daya ya tsere daga wurin.