- Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Hon Nasir Isa Kwarra ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya kudurin gwamnati mai ci na samar da sahihan bayanan yawan jama’a
- Tuni Hukumar ta kammala siyan kayan da suka dace domin kidayar yawan jama’a da gidaje da ake shirin yi
- Tuni hukumar ta gano wasu mutane na musamman da ba sa zama a gidajen su na asali
Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Hon Nasir Isa Kwarra, a ranar Litinin ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya kudurin gwamnati mai ci na samar da sahihan bayanan yawan jama’a da aka kiyasta a halin yanzu miliyan 223, Tribune Online ta rahoto.
Hon Kwara ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kafafen yada labarai bayan wata ganawa da ya yi da ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr Betta Edu, wadda ta bayyana muhimmancin bayanan da za su taimaka wajen isar da ajandar sabunta fata na wannan gwamnati.
KARANTA WANNAN: NFF ta Dakatar da Wasu Alkalan Wasa 14 Kan Abu 1
A cewarsa, hukumar ta kuma gano wasu mutane na musamman da ba sa zama a gidajen da aka saba, wadanda suka hada da ‘yan gudun hijira (IDPs), masunta, makiyaya, da wadanda ke zaune a karkashin gadoji da dai sauransu.
Ya bayyana cewa tuni Hukumar ta kammala siyan kayan da suka dace domin kidayar yawan jama’a da gidaje masu zuwa, ya kara da cewa hukumar ta kebe kananan hukumomi 774 dake fadin kasar nan kuma tana da taswirorin wuraren zama, ofisoshi, tashoshin ruwa da dai sauransu.
Da yake amsa tambayoyi game da ainihin adadin mutanen, Hon Kwarra ya ce, “Eh, ita (Ministar) ta yi wannan tambayar, kuma ina ganin tambaya ce mai jagora. Ya zuwa yanzu, ba mu da ainihin adadin mutanen da muke da su. Abin da muke da shi shine kawai kimantawa.
“Mun yi hasashe da yawa, tun daga kidayar da ta gabata zuwa yawan jama’a, kuma mun yi imanin cewa an kiyasta mu miliyan 223 ne a Najeriya.
Yana da kimanta; hasashe ne. Amma don samun ainihin adadi, muna buƙatar gudanar da ƙidayar jama’a. Muna da burin samarwa al’ummar Nijeriya, gwamnatin Nijeriya, da al’ummar duniya ainihin yawan al’ummar Nijeriya, halayenta, rarrabawarta, da dai sauransu.
Sannan “Muna bukatar ’yan Najeriya su tallafa mana yayin da muke gudanar da shirye-shiryen gudanar da kidayar jama’a.
Kamar yadda ta ambata, muna kuma adana bayanai masu yawa da za mu iya amfani da su saboda ana samun su ta hanyar amfani da GIS, GPS, da hotunan tauraron dan adam.
“Don haka, yayi daidai sosai. Tare da ingantaccen tsarin kowane gini, kowane kayan aiki a wannan ƙasa, har ma da wuraren ruwa da muke da su, rarraba yawan jama’a, matsakaicin girman iyali, da sauransu.
“Akwai abubuwan da za mu iya amfani da su da zarar mun kammala ƙidayar. An riga an sami bayanan kasa na wuraren, kuma za mu iya amfani da su kafin gudanar da ƙidayar jama’a na gaba, “in ji shugaban NPC.
NPC Ta Musanta Zargin Yi Mata Kutse A Ma’adar Bayananta
Yayin da yake amsa tambayoyi dangane da rahotannin da ake zargin an yi wa hukumar NPC kutse don satar bayanai Hon. Kwara, wanda ya yi watsi da rahoton, ya ce rahoton ba shi da tushe balle makama.
Ya ce, “Muna da dukkan matakan da aka dauka. Wannan labarin kutse an yi shi ne kawai. Ba gaskiya ba ne. Babu wani kutse da akayi mana ko kadan.
“Bayananmu suna da tsaro sosai. Koyaya, har yanzu muna ginawa da ƙarfafa tsaro a kusa da bayananmu. Tare da amincewar gwamnati, muna son gina Cibiyar Tsaro ta yanar gizo wacce ba kawai za ta jira har sai an kai muku hari ba amma za ta fara farautar duk wani abin da ya faru, don haka za a kiyaye bayanan da muka bude da kyau.”
A nata jawabin, ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr Betta Edu, ta kalubalanci hukumar NPC kan bukatar samar da sahihin bayanan yawan mutanen da za su taimaka wajen tsarawa da aiwatar da aikin ma’aikatar.
Dokta Edu ta ce, “Muna da shugaban hukumar da daukacin tawagar daga hukumar kidaya ta kasa a ma’aikatar da ke neman hadin gwiwa da ma’aikatar.
“Su ne masu kula da bayanan da muke da su a Najeriya, don haka su ke ajiye bayanan kidayar jama’a da sauran muhimman bayanai masu muhimmanci wajen isar da wa’adinmu, wanda shi ne ajandar sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Mafi mahimmanci, za su yi aiki tare da mu tun daga tushe, musamman game da aiwatarwa, sa ido, da kimantawa. Suna da ma’aikata a ƙasa a yankuna daban-daban, ƙananan hukumomi, da al’ummomi, kuma waɗannan ma’aikatan za su yi aiki tare da mu.
“Za mu kafa ƙungiyar fasaha tsakanin Ma’aikatar da Hukumar don fitar da sassa daban-daban na wannan haɗin gwiwar.
“Bugu da ƙari, za mu yi aiki tare da ƙungiyarsu kan taswirar zamani ta kasa da kididdiga a duk faɗin ƙasar.
“Hakan zai taimaka wajen cikakken aiwatar da ma’aikatar Yaki da Talauci da al’amuran jin kai a fadin kasar baki daya. Abokiyar tarayya ce mai inganci, kuma za mu tallafa musu gaba daya,” in ji ta.
A wani labarin kuma, Rundunar ‘Yan Sanda Za ta Tura Jami’ai 40k Domin Samar Da Tsaro a Zaben Gwamnan Kogi
Rundunar ‘yan sandan Kogi ta ce tana shirin tura jami’an ‘yan sanda sama da dubu 40,000 a fadin jihar domin tabbatar da gudanar da zaben gwamna cikin lumana
Kasancewar isassun jami’an tsaro a jihar, ana kira ga kowa da kowa ya fito ya yi amfani da ‘yancinsa domin kada kuri’a
An umarci jami’an tsaron da su yi adalci ga kowa saboda sun je jihar ne don yi wa jama’a hidima ba wani mutum ba
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta ce tana shirin tura jami’an ‘yan sanda sama da dubu 40,000 a fadin jihar domin tabbatar da gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba cikin lumana.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP, Bethrand Onuoha, ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Lokoja ranar Litinin.