- Matan shugaban karamar hukumar Kiyawa biyu a jihar Jigawa da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, sun shaki iskar ‘yanci
- Barayi da dama sun kai farmaki gidan ciyaman din tare da sace matan shugaban karamar hukumar su biyu
- Tuni matan shugaban karamar hukumar suka sake haduwa da danginsu
Matan shugaban karamar hukumar Kiyawa biyu a jihar Jigawa da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da su, sun shaki iskar ‘yanci.
Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da sakin su a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Tarayya Ta Kwaso Bakin Haure 161 ‘Yan Najeriya Da Suka Makale a Libya
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa ‘yan bindiga da dama sun kai farmaki gidansu tare da yin garkuwa da matan shugaban karamar hukumar su biyu a daren Juma’a.
A cewar sanarwar, “Masu garkuwa sun sako matan shugaban karamar hukumar Kiyawa biyu a karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.”
Sanarwar ta tabbatar da cewa tun daga lokacin suka sake haduwa da danginsu, amma duk da haka, sun yi shiru kan ko ‘yan sanda sun ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ko kuma an ba ‘yan fashin kudin fansa domin su samu ‘yancinsu.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa DAILY POST cewa lallai an biya kudin fansa kafin a sako su.
A wani labarin kuma, Shugaba Tinubu Ya Yi Wasu Sabbin Nade-Nade a Gwamnatinsa Bayanai Sun Fito
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabbin kwamishinonin zartarwa guda uku a Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya NUPRC
Bayanan nadin na kushe ta cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ngelale ya fitar
Shugaban kasar ya amince da wannan sake fasalin bisa la’akari da zurfin saninsa game da duk abubuwan da suka shafi fannin da nufin kafa tsari da al’adu wanda ke kawar da mummunar dabi’a
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabbin kwamishinonin zartarwa guda uku tare da amincewa da sake tura wani da ake da shi na Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NUPRC).
Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ajuri Ngelale ya fitar ta sanar da wadanda aka nada sun hada da Bashir Indabawa, Dakta Kelechi Ofoegbu, Enorense Amadasu, da Babajide Fasina.