- Kocin Manchester City, Guardiola, ya ce Erling Haaland zai lashe kyautar Ballon d’Or ne kawai idan ya ci gaba da zira kwallo da cin kofuna
- Dan wasan a yanzu yawan kwallayen da ya ci a kakar wasa sun kai zuwa 15 a wasanni da dama
- Idan shi da abokansa za su iya lashe kofuna da yawa, to zai samu damar lashe ta
Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce Erling Haaland zai lashe kyautar Ballon d’Or ne kawai idan ya ci gaba da zira kwallo da cin kofuna.
Guardiola yana magana ne bayan Haaland ya zura kwallaye biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da suka doke Young Boys a daren Talata.
KARANTA WANNAN: Matar Aure Ta Nemi Saki Kan Niyyar Mijinta Na Cefanar da Gidansa Ya Karo Aure
Dan wasan mai shekaru 23 a yanzu yawan kwallayen da ya ci a kakar wasa sun kai zuwa 15 a wasanni da dama.
A bana, Haaland ya zo na biyu a gaban Lionel Messi, amma an tambayi Guardiola ko dan wasan mai shekaru 23 zai iya daukaka kyautar a shekara mai zuwa.
“Idan shi da abokansa za su iya lashe kofuna da yawa, to zai samu damar lashe ta.
“Idan bai yi ba, to ba zai yi nasara ba,” in ji Guardiola.
Haaland yanzu yana da kwallaye 39 a wasanni 34 na gasar zakarun Turai kuma yanzu ya ci 67 a wasanni 70 da City ta buga.
A wani labarin kuma, Zabukan Jihohin Kogi, Bayelsa Da Imo: IPC Ta Horar da ‘Yan Jarida 80
Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa IPC ta horar da ‘yan jarida maza da mata daga jihohin Kogi, Bayelsa, da kuma Imo
Taron bitar ya kasance wani bangare ne na ayyukan da ake yi a karkashin shirin IPC na bada sahihan bayan zabe masu inganci ga ‘yan Kasa
Mahalarta taron sun kuma amince da tabbatar da sahihancin rahotannin zabe, musamman ta hanyar ajiye son zuciya don magance rikice-rikice
Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa IPC ta horar da ‘yan jarida maza da mata daga jihohin Kogi, Bayelsa, da Imo gabanin gudanar da zaben gwamna.
Horarwar ta kunshi kafafen yada labarai, jaridu na bugawa, da kuma kafafen yada labarai na yanar gizo a jihohi ukun da zasu bayar da rahotanni kan yadda zabubbukan za su kasance a ranar 11 ga watan Nuwamba.