- Shugaban kasa Bola Tinubu ya baiwa hukumar kidaya ta kasa NPC tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya wajen gudanar da kidayar jama’a a kasar nan
- Al’ummar Najeriya ba za su iya yin kasa a gwiwa ba wajen samar da bayanai masu inganci
- Gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari ta saki zunzurutun kudi har naira biliyan 200 ga hukumar kidayar jama’a domin gudanar da kidayar ‘yan Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu ya baiwa hukumar kidaya ta kasa NPC tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya wajen gudanar da kidayar jama’a a kasar nan, Daily Post ta rawaito.
Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Laraba, a wajen taron kaddamar da asusun ajiyar bayanai na kasa, Digital CRVS System da kuma kaddamar da kwamitin kula da CRVS na kasa a fadar shugaban kasa ta Villa dake Abuja.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: EFCC ta Tabi Umarni Kotu,Ta Gurfanar da Emefiele a Gaban Kotu
Yayin da yake kira da a hada kai a tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati, Tinubu ya jaddada muhimmancin bayanai ga ci gaban kasa.
Ya yi kira ga kwararrun masu kidayar jama’a da su tura fasahohin zamani wajen tattara bayanai kan yawan al’ummar Najeriya, yana mai cewa al’ummar kasar ba za su iya yin kasa a gwiwa ba wajen samar da bayanai masu inganci.
A cewar shugaban kasar Najeriya na da matukar godiya domin ba ta iya fuskantar bala’o’i.
Idan zaku iya tuna cewa gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari ta saki zunzurutun kudi har naira biliyan 200 ga hukumar kidayar jama’a domin gudanar da kidayar ‘yan Najeriya.
Yayin da hukumar ta tura kaso mai yawa na kudaden a matakin farko na kidayar jama’a, gwamnatin tarayya ta dage atisayen ne saboda wasu wuraren da aka fita.
A wani labarin kuma, EFCC ta Gurfanar da Daliban Jami’ar OAU su 11 a Gaban Kotu Bisa Zargin Zamba
Hukumar EFCC shiyyar Ibadan ta gurfanar da wasu dalibai 11 na jami’ar Obafemi Awolowo, OAU, a gaban mai shari’a Nathaniel Ayo-Emmanuel na babbar kotun tarayya dake Osogbo bisa zarginsu da hannu a zamba ta intanet
An gurfanar da tara daga cikin wadanda ake tuhumar a kan tuhume-tuhume daya, yayin da sauran biyun kan tuhume-tuhume guda shida
Tuni wadanda ake tuhuma wasu suka sami beli ya yin da wasu suka tafi gidan yari
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Ibadan ta gurfanar da wasu dalibai 11 na jami’ar Obafemi Awolowo, OAU, a gaban mai shari’a Nathaniel Ayo-Emmanuel na babbar kotun tarayya dake Osogbo, jihar Osun bisa zarginsu da hannu a zamba ta intanet.
An gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume daban-daban daga daya zuwa shida kamar yadda EFCC ta fi son a kan su.