- Yanzu haka dai kasar Isra’ila ta amince da aiwatar da tsagaita bude wuta na tsawon sa’o’i hudu a kowace rana a yankin arewacin Zirin Gaza a cewar fadar White House
- Tuni dai wannan sanarwa ta fara aiki nan take
- A ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, rikici dauke da makamai ya barke tsakanin Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa karkashin jagorancin Hamas
Kusan wata guda bayan fara wani kazamin yaki tsakanin sojojin Isra’ila da mayakan Hamas, Isra’ila ta amince da aiwatar da tsagaita bude wuta na tsawon sa’o’i hudu a kowace rana a yankin arewacin Gaza, in ji fadar White House.
Kakakin Majalisar Tsaro na Fadar White House John Kirby ya ce za a ba da sanarwar sa’o’i uku kafin nan.
KARANTA WANNAN: Zaben Kogi: Atiku Ya Bukaci Masu Kada Kuri’a Su Dongwalawa dan Takarar Gwamnan PDP
Ya ce: “Isra’ilawa sun gaya mana cewa ba za a yi wani farmakin soji a wadannan yankunan ba a tsawon lokacin da aka dakatar kuma wannan aikin ya fara ne a yau.”
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, rikici dauke da makamai ya barke tsakanin Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa karkashin jagorancin Hamas daga zirin Gaza bayan da sojojin suka kaddamar da farmaki ta bangarori da dama na Kudancin Isra’ila.
Rahotanni sun ce akalla Falasdinawa 10,812 aka hallaka a yakin Zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Karin Kasafin Kudin N2.17tr
Yanzu haka dai Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan karin kasafin kudi Naira tiriliyan 2.17 na 2023
A kwanakin baya ne dai majalisar dattawa ta amince da karin kasafin kudin
Bikin rattaba hannun na shugaba Tinubu ya samu halartar kososhin gwamnatin tarayya
Yanzu haka dai Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan karin kasafin kudi Naira tiriliyan 2.17 na 2023, wanda majalisar dokokin kasar ta amince da shi kwanan nan.
Yayin da ya rattaba hannu kan dokar karin kasafin kudi na shekarar 2023 a fadar gwamnati da yammacin yau, shugaba Tinubu ya sa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abass suka halarta.