- Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Imo,Sanata Samuel Anyanwu ya koka kan wasu kura-kurai da ake zargin an yi a zaben
- Dan takarar yi kira da a soke sakamakon zaben a yankunan da ake zargin ‘yan daba sun haifar da tashe-tashen hankula
- Ya kamata INEC ta yi la’akari da shaidun da ake da su tare da soke sakamakon zabe a yankunan da abin ya shafa
Sanata Samuel Anyanwu, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Imo, ya koka kan wasu kura-kurai da ake zargin an yi a zaben na ranar Asabar, Daily Post ta rawaito.
A yayin da yake magana kan rahotannin wakilan jam’iyyar na wuraren zabe, Anyanwu ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai a wasu rumfunan zabe da suka hada da sace akwatin zabe, sayen kuri’u da dai sauransu.
KARANTA WANNAN: ‘Wanda Zai Aureni Ya Girmeni da Shekaru 30 Shi Yasa Naki Aurensa’ — Budurwa
Ya yi wannan ikirarin ne a wata hira da manema labarai a gidansa na Amaimo da ke karamar hukumar Ikeduru ta Imo.
Anyanwu ya kuma yi kira da a soke sakamakon zaben a yankunan da ake zargin ‘yan daba sun haifar da tashe-tashen hankula.
Ya kuma bukaci INEC da “Ta haska hasken bincikenta a karamar hukumar Ikeduru”.
Anyanwu ya ce: “Ina da shaidar cewa daya daga cikin ‘yan barandan na dan majalisar ne.
“A cikin shirin kwace akwatunan zabe, katin shaidar dan majalisar ya fadi kuma ina da shi a nan tare da ni.
“Ina kira ga INEC da ta yi la’akari da shaidun da ake da su tare da soke sakamakon zabe a yankunan da abin ya shafa.”
A wani labarin kuma, Dalilin da Ya Sa Muka Dakatar da Ayyukan Ilimi a Makarantun Sakandaren Taraba – ASUSS
Shugabancin kungiyar malaman makarantun sakandire, ASUSS ya dakatar da harkokin ilimi a makarantun sakandire a fadin jihar Taraba
Matakin dai na nuna adawa da kisan gillar da wasu da ake zargin dalibai ne suka yi wa abokin aikinsu
Hanya mafi kyau da za mu bayyana bakin cikinmu ga gwamnati, iyaye da masu ruwa da tsaki, ita ce mu gaya wa mambobinmu su dakatar da ayyukan ilimi
Shugabancin kungiyar malaman makarantun sakandire, ASUSS ya dakatar da harkokin ilimi a makarantun sakandire a fadin jihar Taraba.
Matakin dai na nuna adawa da kisan gillar da wasu da ake zargin dalibai ne suka yi wa abokin aikinsu.