- Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum mai suna George Sibo ya mutu a Twon-Brass, hedkwatar karamar hukumar Brass a jihar Bayelsa
- Tuni akayi Allah wadai da farmakin kan Wanda abin ya afkawa
- Dole ne jami’an tsaro su gaggauta kama wadanda suka aikata laifin tare da hukunta su
Yanzu haka dai rahotanni sun bayyana cewa wani mutum mai suna George Sibo ya mutu ranar Lahadi da rana a Twon-Brass, hedkwatar karamar hukumar Brass a jihar Bayelsa bayan da wasu gungun ’yan daba suka kai masa hari, Punch ta rawaito.
An tattaro cewa an kai wa marigayin hari ne a cibiyar tattara sakamakon zaben gwamna da ke hedikwatar karamar hukumar a lokacin da ake mika sakamakon wasu mazabu 2.
KARANTA WANNAN: Zaben Kogi: INEC Na Shan Suka Kan Yadda Ta Cigaba da Tattara Sakamakon Zabe Duk da Cushen Kuri’u
Sibo, wanda aka fi sani da “Kobo-Kobo” an ce dan kabilar Twon-Brass ne kuma mai taimaka wa wani dan siyasa daga karamar hukumar.
Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Brass 1, Daniel Charles, ya yi Allah wadai da kisan.
Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su gaggauta kama wadanda suka aikata laifin tare da hukunta su.
Charles ya yi mamakin dalilin da yasa masu burin yin mulki za su ji daɗin tashin hankali.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Asinim Butswat, ya ce yana jiran cikakken bayani daga kwamandan yankin na karamar hukumar Brass.
A wani labarin kuma, Gwamnan Jahar Kwara Ya Jajantawa Iyalin Samanja Mazan Fama
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a ranar Lahadi, ya bayyana rasuwar Alh. Usman Baba Patigi (Samanja) a matsayin karshen babban zamani a masana’antar barkwanci ta Najeriya, musamman a arewacin Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Rafiu Ajakaye ya sanyawa hannu, wadda kwafinta aka aikewa LEADERSHIP.