- Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma TUC sun kaddamar da yajin aikin a fadin kasa
- Duk da umarni kotun masana’antu na haramtawa NLC tsunduma yajin aikin sai da ta tafi
- NLC ta umarci mambobinta da su fara yajin aikin gama gari a fadin kasar sakamakon harin da aka kai wa shugaban kungiyar, Ajaero
Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma TUC sun kaddamar da yajin aikin a fadin kasa, Daily Post ta rawaito.
Kungiyar kwadago ta NLC ta umarci mambobinta da su fara yajin aikin gama gari a fadin kasar sakamakon harin da aka kai wa shugaban kungiyar, Joe Ajaero.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: WAEC ta Kaddamar CBT don Gudanar da Jarabawar SSCE
Kungiyar kwadagon ta umurci abokan huldarta da su aiwatar da kudurorin majalisar zartarwa ta kasa.
Shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin.
Osifo ya ce yajin aikin zai ci gaba da kasancewa har sai “gwamnati a dukkan matakai sun farga da alhakin da ya rataya a wuyansu.”
A makon da ya gabata, Kungiyar Kwadago ta ayyana yajin aikin gama gari a fadin kasar daga ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, 2023.
A wani labarin kuma, Gwamna Douye Diri Na Jam’iyar PDP Ya Lashe Zaben Jahar Bayelsa
Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya lashe zaben ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Nasarar Diri da ba za a iya mantawa da shi ba ta bayyana bayan tattara sakamakon zaben daga dukkan kananan hukumomi takwas na jihar a ranar Litinin da yamma.