- Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce tsofaffin takardun kudin Naira za su ci gaba da zama kan doka
- A baya CBN ya gabatar da sake fasalin Naira N200, N500 da N1,000 a watan Oktobar shekarar 2022 kuma an sanya wasu wa’adin da za a daina karbar tsofaffin takardun kudin
- CBN na aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin su janye hukuncin kotun da ke kan wannan batu
Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce tsofaffin takardun kudin Naira za su ci gaba da zama a kan doka.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa babban bakin Najeriya CBN ya gabatar da sake fasalin Naira N200, N500 da N1,000 a watan Oktobar shekarar 2022 kuma an sanya wasu wa’adin da za a daina karbar tsofaffin takardun kudin.
KARANTA WANNAN: Uwargidan Shugaban Kasa Ta Gabatar da Tsabar Kudi N427m Ga Matan Jaruman Da Suka Mutu
Amma a ranar Talata, CBN ya sanar da jama’a bukatarsa na tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun kudin Naira N200, N500 da N1,000.
“Wannan ya yi daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya da kuma hana maimaita abubuwan da suka faru a baya,” in ji sanarwar da Isa AbdulMumin, Daraktan Sadarwa na CBN, ya sanyawa hannu.
“Don haka duk takardun kudin da babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar, bisa ga sashe na 20(5) na dokar CBN ta shekarar 2007, za su ci gaba da zama doka har sai baba ta gani wanda zai wuce wa’adin farko na ranar 31 ga watan Disamba, 2023. .
“Babban bankin Najeriya na aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin su janye hukuncin kotun da ke kan wannan batu.
“Saboda haka, dukkan rassan CBN a fadin kasar nan za su ci gaba da fitarwa da karban duk takardun kudi na banki na Najeriya, tsofaffi da wadanda aka canza su da kuma daga bankunan ajiya (DMBS).
“An umurci jama’a da su ci gaba da karbar duk wata (tsohuwar takardar Naira ko wacce aka sakewa fasali) don yin mu’amala ta yau da kullum tare da kula da wadannan takardun kudi da matukar kulawa, don kiyayewa da kuma kare rayuwar kudaden.
“Har ila yau, ana ƙarfafa jama’a da su rungumi madadin hanyoyin biyan kuɗi, e-channels, don
mu’amalar yau da kullum,” inji shi.
A wani labarin kuma, Gwamna Inuwa Ya Yaba da Gagarumar Nasarar Da APC ta Samu a Imo da Kogi
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya takwaransa na Imo, Hope Uzodinma, da kuma zababben gwamnan Kogi, Usman Ahmed Ododo murnar nasarar da suka samu a zaben gwamna
Wannan gagarumar nasara ta tabbatar da amincewar jama’a ga gwamnatin APC
Wannan wa’adin wata dama ce da za ta ginu a kan tushen ci gaba da wadata da aka riga aka shimfida a jihohin biyu
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya takwaransa na jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, da kuma zababben gwamnan jihar Kogi, Usman Ahmed Ododo murnar nasarar da suka samu a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Gwamnan wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, ya ce nasarar da ‘yan takarar jam’iyyar APC suka samu a jihohin biyu ya nuna farin jini da kuma amincewar da jama’a ke da shi a jam’iyyar mai mulki.