- A halin yanzu gwamnatin tarayyar Najeriya na gudanar da wani taro da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC kan yajin aikin da suke yi
- Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da aka kai wa shugaban NLC hari a Owerri, babban birnin jihar Imo
- Tuni dai manyan jami’an gwamnati dana kwadago suka halarci taron
A halin yanzu gwamnatin tarayyar Najeriya na gudanar da wani taro da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC kan yajin aikin da suke yi a fadin kasar.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa taron na gudana ne a ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA.
Ggg
KARANTA WANNAN: Zaben Gwamnan Kogi Da Muka Gudanar Sahihine — INEC ta Tabbatar
Wadanda suka hallarci taron sun hada da ministan kwadago Simon Bako Lalong, karamin minista Hon. Nkeiruka Onyeajeocha da NSA Nuhu Ribadu.
Haka kuma shugabannin kungiyar kwadago karkashin jagorancin shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo, da babban sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja da sauran shugabannin kungiyar kwadagon sun halarci taron.
Ku tuna cewa NLC da TUC, sun kaddamar da yajin aikin a duk fadin kasar, inda suka bukaci a kama wadanda ake zargin ‘yan daba da masu daukar nauyinsu wadanda suka farmaki Shugaban kungiyar.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da aka kai wa shugaban NLC hari a Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar 1 ga watan Nuwamba lokacin da ma’aikata a jihar suka gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu albashi.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Hilla Kasar Waje Domin Hakartar Wani Muhimmin Taro
Shugaban kasa Bola Tinubu zai bi sahun sauran shugabannin kasashe a birnin Bissau na kasar Guinea-Bissau, domin halartar bikin cikar kasar shekaru 50
Guinea-Bissau tana bikin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai a ranar 24 ga watan Satumba, 2023
Bisa hakan kasar ta sanya sabuwar rana domin gudanar da bukukuwan ranar samun ‘yancin kai
Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Alhamis zai bi sahun sauran shugabannin kasashe a birnin Bissau na kasar Guinea-Bissau, domin halartar bikin cikar kasar shekaru 50 da samun ‘yancin kai da kuma ranar sojoji.
A cewar wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Laraba, shugaban kasar zai isa birnin Bissau a ranar Alhamis domin gudanar da bikin wanda shugaba Umaro Sissoco Embalo zai karbi bakuncinsa.