- Jam’iyyar PDP a hukumance ta bayyana jaddawalin da zasu jagoranci gudanar da wasu ayyuka tun kafin zaben gwamnan Edo
- Tuni jam’iyyar PDP ta bayyana lokacin da za a gudanar da taron tantance dan takarar gwamna jihar
- Dole ne duk wani dan takarar da ke neman wannan mukami da su samu fom din tsayawa takara a kan Naira miliyan 21
Jam’iyyar PDP a hukumance ta bayyana jaddawalin da zasu jagoranci gudanar da wasu ayyuka tun kafin zaben gwamnan jihar Edo, Daily Post ta rawaito.
Kwamitin gudanarwa na kasa ne ya fitar da jadawalin a ranar Alhamis bayan wani taron hadin gwiwa na kwamitin amintattu da kwamitin zartarwa na kasa a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Gamayyar Kungiyoyin Kwadago Sun Dakatar da Yajin Aikin Gama Gari
A wata sanarwa mai dauke da rattaba hannun sakataren kungiyar na kasa Umar Bature,yace jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za a gudanar da taron tantance dan takarar gwamna a ranar 22 ga watan Fabrairun 2024.
Ana bukatar ‘yan takarar da ke neman wannan mukami da su samu fom din tsayawa takara a kan Naira miliyan 21, tare da rangwamen kashi 50 cikin 100 ga matasa masu shekaru tsakanin 25 zuwa 30.
Jadawalin da aka zayyana ya hada da: 16 ga watan Nuwamba – 7 ga watan Disamba 7: Rijistar tsofaffi da sababbin mambobin jam’iyya shine a ranar 14 ga watan Disamba: Ranar ƙarshe don ƙaddamar da rajistar mazabu zuwa Cibiyar Ƙungiya da Tattarawa.
Taron shawarwari na masu ruwa da tsaki tare da Ƙungiyar gudanarwa ta Ƙasa zai gudana a ranar 19-20 ga watan Disamba.
Siyar da Fom da nuna sha’awa na wucin gadi ga duk ofisoshi zai gudana a ranar 10-16 ga watan Janairu.
Ranar ƙarshe don mikawa da kammala l sha’awa da sayen fom na na wucin gadi zai gudana a ranar 17 ga watan Janairu.
Kwamitin gudanarwa na kasa zai tantance masu neman kujerar gwamna a ranar 18 ga watan Janairun 2024:
Siyar da fom ga yan takara da masu nema da suka kammala zasu mika fom ɗin nuna sha’awa a ranar 19-25 ga watan Janairu.
Ranar ƙarshe don ƙaddamar da cike fom na takara shine a ranar 27 ga watan Janairun 2024.
Kazalika zaben fidda gwani na gwamna zai gudana a ranar 22 ga watan Fabrairu.
24 ga watan Fabrairu zata kasance ranar daukaka kara a zaben fidda gwani na gwamna.
A wani labarin kuma, Bayan Rufewa Ta Wucin Gadi, An Sake Buɗe Sararin Samaniyar Filin Jirgin Saman Fatakwal
An sake bude filin tashi da saukar jiragen sama na Fatakwal da aka rufe sakamakon wani yanayi na gaggawa
Hakan ya biyo bayan wani jirgin sama da ya tsallake rijiya da baya a filin jirgin saman kasa da kasa dake jihar
Yayin da ake ci gaba da kokarin kawar da jiragen da abin ya shafa babu wani jirgi daya isa ya sauka
An sake bude filin tashi da saukar jiragen sama na Fatakwal da aka rufe sakamakon wani yanayi na gaggawa na baya bayan nan daya afku.
Wani jami’in filin jirgin ya shaida wa manema labarai cewa, wani jirgin sama ya tsallake rijiya da baya a filin jirgin saman kasa da kasa ranar Talata.