- Gwamnan Kaduna Uba Sani ya sanar da nadin Jerry Adams a matsayin shugaban hukumar tara haraji ta Kaduna KADIRS
- Sabon shugaban hukumar ya kasance gogagge kuma kwararren mai kula da haraji
- Gwamna Sani ya bukaci sabbin wadanda aka nada su kasance masu himma tare da samar da dabaru da tsare-tsare don ciyar da hukumar ta KADIRS zuwa matsayi mafi girma
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya sanar da nadin Jerry Adams a matsayin shugaban hukumar tara haraji ta Kaduna KADIRS.
Nadin nasa zai fara aiki ne zuwa lokacin da majalisar dokokin jihar Kaduna ta tabbatar da shi.
KARANTA WANNAN: Ban Taba Dandana Barasa da Taba Sigari Ba, In Ji Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kaduna Dakta Abdulkadir Muazu Mayere ya fitar, ta bayyana cewa gwamnan ya kara nada Umar Sani a matsayin sabon darakta mai kula da ayyukan tara kudaden shiga, yayin da Dakta Muhammad Lawal aka mayar da shi mukamin babban darakta a ma’aikatar KADIRS.
Adams, kafin a nada shi a matsayin shugaban riko na KADIRS a watan Yulin 2023, ya kasance Babban Darakta na Ayyukan Kamfanoni kuma yanzu Dakta Lawal zai maye gurbinsa.
A cewar sanarwar: “Jerry Adams gogaggen mai kula da haraji ne, ƙwararren akawu, ƙwararren ci gaban kasuwanci kuma ɗan kasuwa tare da gogewar ƙwarwar sama da shekaru 23.
“Umar Sani, sabon Babban Daraktan Ayyuka na Kudi, ya fito ne daga Karamar Hukumar Zariya, kuma ya kammala karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello da Harvard Centre for International Development.
Yayin da yake taya wadanda aka nada murna, Gwamna Sani ya bukace su da su kasance masu himma tare da samar da dabaru da tsare-tsare don ciyar da hukumar ta KADIRS zuwa matsayi mafi girma.
A wani labarin kuma, Nigeria Vs Lesotho: Super Eagles Ta Kasa Samun Nasara a Wasan Da Suka Buga
Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta kasa doke kasar Lesotho a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026
Lesotho ta fara cin kwallo a ragar Najeriya a minti na 56 da fara wasa
Sai dai tuni Super Eagles ta rama a minti na 67 da fara wasa inda ta zura kwallo a ragar Lesotho
Kungiyar Super Eagles ta Najeriya a yammacin ranar Alhamis ta kasa doke kasar Lesotho a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026.
An tashi wasan ne babu ci 0-0 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo.