- Gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwar sakin fursunoni 4,068 da aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari daban-daban tare da basu zabin biyan tara
- Ministan ya yi kira da a yi gyara a hukumar shari’ar miyagun laifuka domin ba da damar gudanar da shari’a cikin gaggawa bisa dimbin fursunonin da ke gidajen yari suna jiran shari’a
- Ku guji aikata laifuka a duk inda kuka tsinci kanku inji ministan
Gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwar sakin fursunoni 4,068 da aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari daban-daban tare da basu zabin biyan tara da diyya a cibiyoyin da ake tsare da su a fadin kasar.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, shine wanda ya yi bikin sakin fursunonin a cibiyar tsaro ta gidan gyaran Hali da tarbiyya da ke Kuje, Abuja a ranar Asabar, ya ce an yi hakan ne a wani yunkuri na rage cunkoso a gidajen yari a fadin kasar nan tare da sanya su mutunta gyare-gyaren da ya dace da kuma gyara masu laifi a inda suke.
KARANTA WANNAN: Masu Ruwa da Tsakin APC sun Yi Kiran a Soke Zaben Kananan Hukumomin Jihar Taraba
Ya koka da cewa ya zuwa ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba, 2023, akwai fursunoni kusan 80,804 a cikin wuraren da ake tsare dasu guda 253 a fadin kasar, kuma jimillar karfin da aka sanya na cibiyoyin tsare mutane 253 ya kai kasa da 50,000.
Tunji-Ojo ya yi kira da a yi gyara a hukumar shari’ar miyagun laifuka domin ba da damar gudanar da shari’a cikin gaggawa, yana mai nuni da cewa dimbin fursunonin da ke gidajen yari suna jiran shari’a.
A cewarsa, Cibiyar Kula da gidan gyaran hali da tarbiyya ta Kuje, inda aka saki 37 daga cikin fursunonin da suka amfana, tana da ikon rike fursunoni 560, amma a halin yanzu, jimillar fursunoni 730 suna tsare a gidan yarin.
Sannan ya kara da cewa daga cikin fursunoni 730, 565 daga cikinsu suna jiran shari’a.
“Wannan ya nuna cewa wuraren da ake tsare da Masu laifin sun cika makil, wanda hakan ya sa aka fara wannan shiri a yau, wanda aka yi niyya don magance cunkoson da ake fama da shi a cibiyoyin mu da ayyukansu na gyara.
“A yau, mun ba da sanarwar sakin jimillar fursunoni 4,068 da ke zaman gidan yari daban-daban a maimakon tara da/ko diyya,” in ji shi.
Tunji-Ojo ya bayyana cewa galibin fursunonin da ake ba wa ’yanci ’yan kasa ne da ba za su iya biyan tarar su ba kuma suna tsare a gidan yari.
Ministan ya bayyana cewa, wasu masu hannu da shuni da kungiyoyi ne suka tara kudaden da suka kai N585,000,000.00 a matsayin wani bangare na alhakinsu na zamantakewa da nufin sakin fursunonin.
“Saboda haka, duk fursunonin da ke gidajen kurkukun da ke da tara ko biyan diyya da bai wuce Naira miliyan daya ba (N1,000,000.00) sun cancanta kuma za su amfana da wannan karimcin.
“Bugu da kari, mun kuma baiwa kowannen su alawus alawus don ba su damar komawa yankunansu,” in ji shi.
Tunji-Ojo ya bukaci fursunonin da suka amfana da su ga ‘yancinsu da suka samu a matsayin wata dama ta biyu ta sake gyara al’amura, inda ya shawarce su da su guji aikata laifuka, yana mai cewa dole ne kowa ya hada kai da Shugaba Tinubu domin mayar da Najeriya kasa mai girma.
Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa an baiwa fursunonin da suka ci gajiyar horon da ya dace da nufin yin tasiri a rayuwarsu ta hanyar samar musu da ilimin yadda za su dogara da kansu idan aka sallame su, yana mai jaddada cewa gwamnati ba wai kawai ta sake su ne ga makomarsu ba.
Ya kuma yi nuni da cewa horon ya kuma shafi ayyukansu na al’umma da ayyukansu na ’yan kasa da kuma dabarun da za su bi don gujewa sake yin hakan.
“A bisa sabon tsarin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, an baiwa fursunonin da suka amfana damar sake dawowa kan turba madaidaiciya da kuma ba da gudummawa ga ci gaban kasa tamu mai daraja,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Jami’in dan Sanda da Wasu Biyar Sun Jikkata a Rikicin Sarauta
Rahotanni sun bayyana cewa an jikkata mutane shida a Eko-Ende dake karamar hukumar Ifelodun ta jihar Osun
Lamarin ya faru ne bayan zaben Wani basarake da wasu biyar
Tuni wadanda iftila’in ya afkawa aka kwantar dasu a asibiti
Rahotanni sun bayyana cewa an jikkata mutane shida a Eko-Ende dake karamar hukumar Ifelodun ta jihar Osun, yayin da wasu da ake zargin masu wasan wuta ne suka kaddamar da hari a ranar Laraba.
Tribune Online ta tattaro cewa an zabi A Chartered Akanta, Adekunle AbdulWaheed Babatunde a matsayin sabon Oba na Eko-Ende.