- Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana bangaren shari’a a matsayin akwatin gawar dimokradiyya a Najeriya
- Martanin na zuwa ne a dai dai lokacin da Kotun Daukaka Kara ta Tsige Gwamnan Filato Caleb Mutfwang
- Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba inji tsohon Sanatan
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana bangaren shari’a a matsayin akwatin gawar dimokradiyya a Najeriya.
Sanata Sani dai na mayar da martani ne kan hukuncin kotun daukaka kara da ta kori Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato.
KARANTA WANNAN: Gwamna Mutfwang Ya Mayar da Martani Game da Korar da Kotun Daukaka Kara Ta Yi Masa
Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin kotun zaben gwamnan da ta tabbatar da zaben Mutfwang a matsayin gwamnan jihar.
Kotun ta ayyana Dr Nentawe Yilwatda na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar yayin da ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta ba shi sabuwar takardar shaidar cin zabe.
Da yake mayar da martani, Sani ya ce hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba.
Da yake wallafawa a shafin na X, Sani ya rubuta cewa: “Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan nasarar zaben gwamnan jihar Filato abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba sannan abin Allah wadai ne.
“Hasken rana mai faɗi na nufin mutane. Bangaren shari’a ya zama akwatin gawar dimokuradiyya.”
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara ta Kori Gwamnan Filato, Mutfwang
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori gwamnan jihar Filato, Mutfwang Manasseh na jam’iyyar PDP daga ofishin sa
Tuni Kotun ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da ta amince da dan takarar gwamna na jam’iyyar, APC
Hakan ya biyo bayan rashin mutunta umarnin Kotu da PDP tayi
Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Lahadi ta kori gwamnan jihar Filato, Mutfwang Manasseh na jam’iyyar PDP daga ofishin sa.
Ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da ta amince da Nentawe Goshwe na jam’iyyar, APC, a matsayin zababben gwamna mai inganci a zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris.