- Kakakin majalisar dokokin Filato, Moses Thomas Sule da mataimakinsa, Hon Gwottaon sun yi murabus daga mukamansu
- Hakan ya faru ne yayin da majalisar ta zabi sabon kakakin majalisa
- Kawo yanzu Babu cikakken Bayani kan murabus din tsohon Kakakin Majalisar da mataimakinsa
Kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Moses Thomas Sule da mataimakinsa, Hon Gwottaon sun yi murabus daga mukamansu.
Hakan ya faru ne yayin da majalisar ta zabi dan majalisa mai wakiltar Pankshin ta Arewa, Gabriel Dawang, a matsayin sabon kakakin majalisar.
KARANTA WANNAN: Babban Hafsan Soji Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwanaki 3 don karrama Tsohon COAS, Alli
Honarabul Timothy Dantong mai wakiltar mazabar Riyom ne ya zama sabon mataimakin kakakin majalisar.
A wani labarin kuma, Rashin Tsaro: An Haramta Ayyukan Masu Jari Bola da Zirga-Zirga aAdamawa
Al’ummar Wuro-Chekke da ke zaune a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, ta haramta ayyukan masu kwasar ganima wato ‘yan jaribola
Tuni aka umarci jami’an ‘yan banga da shugabannin al’umma da su aiwatar da wannan umarni cikin gaggawa
An haramtawa kowa shiga Cikin garin da karfe 11 na dare sai dai idan an nemi izini kafin a ba su damar shiga
Al’ummar Wuro-Chekke da ke zaune a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, ta haramta wa masu kwasar ganima wato ‘yan jaribola a ko’ina a cikin yankinta.
Haka kuma shugabannin al’ummar sun haramtawa kowa shiga Cikin garin da karfe 11 na dare sai dai idan an nemi izini kafin a ba su damar shiga.