- Dakarun rundunar hadin gwiwa ta shiyyar arewa maso yamma Operation HADARIN DAJI sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su
- Tuni sojojin suka tarwatsa maboyar barayin inda suka ranta Ana kare
- Ceto Mutane ya biyo bayan kai Wani simame da dakarun Soji suka kai
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta shiyyar arewa maso yamma Operation HADARIN DAJI sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su a yankuna daban-daban na jihar Sokoto, a ranar Talata.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X ranar Laraba.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Kaduna Ta Karbe Ayyukan Karamar Hukuma, Ta Dakatar da Kansiloli 8
A cewar sanarwar, sojojin da ke karkashin kwamandan runduna ta 8 ta sojojin Najeriya da ke Sokoto, Manjo Janar Godwin Mutkut, sun ci gaba da kai hare-hare tare da kaddamar da hare-hare a yankunan ‘yan ta’adda da ke yankunan da suke gudanar da ayyukansu a Arewa maso Yamma.
Sanarwar ta kara da cewa, “A wani samame na kwanan nan da dakarun OPHD suka gudanar a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2023 a karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto, sun share kauyen Alya Fulani da ke dajin Buani, inda aka ceto mutane 30 da aka yi garkuwa da su.
“Duk maboyar ‘yan ta’addan da aka gano an lalata su ne yayin da ‘yan ta’addan suka yi watsi da wadanda suka yi garkuwa da su, suka gudu daga sansanonin su kafin isowar sojojin.
“Sojojin sun kuma zarce zuwa kauyen Goboro inda aka ceto wata mace da aka yi garkuwa da ita yayin da ‘yan ta’addan suka gudu cikin rudani saboda karfin wuta na sojoji.”
A wani labarin kuma, Tsohon Mataimakin Gwamna da Wasu Mutane Biyu Sun Fice Daga PDP zuwa APC
Wasu kososhin PDP da jiga-jigan jam’iyyar biyu sun fice daga jam’iyyar sun koma jam’iyyar APC mai mulki
Masu sauya shekar Sun ce salon jagorancin Gwamnan Jihar ne ya Sanya suka koma APC
Tuni APC ta nuna farin cikinta kan wannan Babban kamu da ta yi na Masu sauya sheka
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja da kuma tsohon jakadan Najeriya a kasar Afrika ta kudu, Ahmed Musa Ibeto da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP guda biyu sun fice daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC mai mulki.
Ibrahim Egbo, tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Lapai Agaie ta tarayya da Alhaji Abubakar Azozo, tsohon kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Neja, sune sauran jiga-jigan siyasar biyu da suka bar PDP zuwa APC.